1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jihadi ko neman abin duniya?

June 27, 2014

Matsanancin ra'ayin addini da kuma tara kudi na daga cikin abubuwan da ke angiza da yawa daga cikin Musulmi 'yan ta'adda a Afirka.

https://p.dw.com/p/1CQgc
Krise im Norden von Mali
Hoto: Reuters

Bari mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda a wannan makon ta yi takaitaccen bayani na wani littafi da wakilinta a nahiyar Afirka, Marc Engelhardt ya wallafa mai taken Jihadi a Afirka.

Matsanancin ra'ayin addini da kuma tara kudi na daga cikin abubuwan da ke angiza da yawa daga cikin Musulmi 'yan ta'adda a Afirka. Inda akasari suke fakewa da addini suna aikata manyan laifuka. Jaridar ta ce sabanin farfagandar da ake yadawa a hukumance, addinin Islama ba ya taka muhimmiyar rawa ga 'yan Jihadi a kasashe irinsu Mali, Somaliya da kuma Najeriya. A matakin farko wadannan kungiyoyi sun fi karkata ga kudi da kuma wasu hada-hada. Mawallafin littafin ya ce ba kungiyoyin Musulmi ne kawai ke fakewa da addini ba, inda ya ba da misali da kungiyar Lord's Resistance Army ta kasar Yuganda wadda aikace-aikacenta suka saba wa karantarwa addinin Kirista. Duk wadannan kungiyoyi suna gudanar da haramtattun harkokin kasuwanci kamar fataucin miyagun kwayoyi, safarar dan Adam, fashi da makami da fashi a teku don samun kudaden tafiyar da harkokinsu.

Rundunar Jamus ta Bundeswehr a Mali

Sojojin Jamus za su ci gaba da zama a Mali, inji jaridar Die Tageszeitung tana mai mayar da hankali ga kuri'ar da majalisar dokokin Jamus ta kada inda ta amince da tsawaita wa'adin aikin sojojin kasar a Mali da shekara guda.

Von der Leyen besucht Soldaten in Mali
Ministar tsaron Jamus von der Leyen lokacin ziyarar da a kai wa sojojin kasar a MaliHoto: Reuters

Yanzu haka dai Jamus na da sojoji 230 karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya, 170 a Mali, inda suke horas da sojojin kasar. A ziyarar da ta kai Amirka makon da ya gabata ministar tsaron Jamus Ursua von der Leyen ta yi alkawarin karfafa shigar da sojin kasarta cikin ayyukan Majalisar Dinkin Duniya. Sai dai duk wanda ya yi zaton Jamus za ta kara yawan sojojinta a ketare to ya yaudari kansa ne, domin abin da ministar ke nufi shi ne taimakon fasaha da kuma daidaikun sojoji.

Ebola a Yammacin Afirka

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a wannan makon tsokaci ta yi game da annobar cutar Ebola wadda ta ce na barazanar gagarar kundila.

Guinea Konacry Ebola Virus
Kamfen wayar da kan jama'a game da cutar EbolaHoto: picture-alliance/AP Photo

Ta ce kungiyar likitoci masu ba da agaji ta nuna cewa yanzu haka annobar Ebola ta zama gagarabadau a yankin yammacin Afirka. A kasashen Liberiya, Saliyo da kuma Guinea ana ci gaba da samun mutane da ke kamuwa da kwayoyin cutar. Tun barkewar cutar a Guinea a farkon wannan shekara mutane 567 suka kamu da ita, sannan 350 tuni suka rigamu gidan gaskiya, inda a Guinea kadai ta yi ajalin mutane 267. Wadannan alkalumman na nuna cewa annobar Ebola a Afirka ta Yamma na zama mafi muni wajen kashe mutane tun gano kwayoyin cutar a shekarar 1976.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe