1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jiga-jigan 'yan siyasar Ivory Coast za su gana

July 27, 2021

A karo na farko tun bayan da bangarorin biyu suka gwabza fada na bayan zabe shekaru 10 da suka gabata, Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara zai gana da Lauren Gbagbo.

https://p.dw.com/p/3y6qC
Bildkombo l Elfenbeinküste l Präsident  Ouattara und ehemaliger Präsident Ghagbo
Hoto: Issouf Sanogo, Sia Kambou/AFP

Masu sharhi na ganin cewa ta yiwu ganawar na nufin abokan hammayar sun mayar da wukakensu cikin kube ne, tare da fatan hakan ka rage radadin zubar da jinin da aka yi a kasar a bara. Sai dai kuma kakakin Gbagbo Justin Katinan Kone na cewa kada mutane su yi tsammanin wani gagarumin al'amari don wannan ziyara ce kawai ta ban girma ga dattijai, idan har hakan zai saukaka yanayi na siyasa. A watan da ya gabata ne dai Gbagbo mai shekarau 76 ya koma kasar daga Turai bayan samun nasara a wata shari'a a Kotun hukunta manya laifuka ta duniya ICC. Rikici dai ya barke a kasar tun bayan da Gbagbo ya ki amincewa da shan kaye a zaben shugaban kasa da ya baiwa Ouattara nasara, lamarin da yayi sanadiyar dubban rayuka.