1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin Shugaban Ghana a gaban majalisa

February 21, 2013

John Dramani Mahama ya tabbatar da shirin daukan tsauraran matakai, domin shawo kan matsalolin da kasar ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/17jeI
Ghanaian President John Mahama raises the staff of office after swearing to an oath of office at the Independence Square, Accra in January 7. 2013. Ghanaian President John Dramani Mahama has been sworn-in into office despite a court challenge by the main opposition New Patriotic party, citing alleged voting fraud resulting in the absence of party officials at the swearing-in ceremony attended by nine heads of state. AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Hoto: Getty Images /AFP

Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya tabbatar da shirin daukan tsauraran matakai, domin shawo kan matsalolin makamashi da kasar ke fuskanta nan da watanni masu zuwa. Shugaba Mahama ya bayyana haka cikin jawabi kan halin da kasar ciki da ya gabatar a gaban majalisar dokoki.

Wannan ya zama jawabi na farko kan halin da kasa ke ciki da Shugaba John Dramani Mahama ya gabatar tun lokacin da ya zama shugaban kasar ta Ghana da ke yankin yammacin Afirka. Jawabin ya zo lokacin da al'umar kasar ke nuna rashin jin dadi da tashin farashin man fetur da yawan katse hasken wutar lantarki gami da rashin samun iseshshen ruwan sha. Shugaba Mahama ya nuna bakin ciki kan halin da ake ciki, sannan ya yi alkawarin daukan matakai da su ka hada da gudanar da aiki yanzu haka cikin magance matsalar katse hasken wutar ta lantarki:

Shugaban ya ce, ''Abun da zai zama mana nasara wajen bunkasa samun haske wutar lantarki amma wani abun bakin ciki shi ne faruwar wasu abubuwa da ba ayi zato ba. Aiki kan bututun gas na yankin yammacin Afirka yanzu an shirya kammalawa zuwa watan Afrilu na wannan shekara ta 2013.''

-Bildrechte für Bilder Nr 2: Anneselma Bentil (asbarber@citizenkofi.com. tel: 00233 267858820) erlaubt der DW diese Bilder zu verwenden. Beschreibung (Bild 2): Gebäude Citizen Kofi entertainment centre im Herzen der ghanaischen Hautstadt, Accra Zulieferer: Eric Segueda
Hoto: Anneselma Bentil

Shugaban Mahama ya kuma nuna rashin jin dadi kan ayar dokar da ta kara albashin manyan jami'an gwamnati fiye da kima, wanda ya janyo gibi kasar ta fuskanci gibin kasafin kudi na kashi kashi 12.1 cikin 100 a shekarar da ta gabata. Daya daga cikin dalilan gyara bisa kudaden jami'an gwamnatin shi ne, domin bunkasa gudumawar da su ke bayarwa.

Ya kara da cewa, ''Yayin da mu ke gaba da mika wuya wajen bunkasa da'ar jami'an gwamnatin Ghana, wadanda kudin da su ke samu bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da masu zaman kansu, saboda wannan mu ka kawo gyara kan albashi, domin samun daidato, hazaka da kuma kara kwazon aiki. Yanzu muna fuskantar kalubalen tabbatar da cewa kudaden da aka kara na karkashin garambawul ga jami'ai bai zama nauyi ba kan kudade al'uma da kuma samun daidaiton tattalin arzikin kasa.''

'Yan majalisa daga bangaren 'yan adawa sun kauracewa jawabin shugaban kasar ta Ghana John Dramani Mahama, saboda yadda su ke kalubalantar sahihancin sakamakon zaben da ya kawo shi kan madafun iko.

Tuni wasu 'yan kasar su ka mayar da martani kan jawabin. Wannan dan dan kasar ga abun da ya ce, ''Akan maganar albashi wannan shi ne karon farko da shugaban kasa ko wani daga bangaren zartaswa ya yi magana kan albashi.''

Alle Bilder von unserer Korrespondentin, Marine Olivesi zur freien Verfügung. gemacht: alle in Nkoranza, Ghana, October 2012 DORF Nkoranza IN GHANA: "NO GHANA": Located in Ghana's deep countryside, Nkoranza used to be nicknamed "No Ghana" by its residents because the town seemed cut off from the rest of the country. Over the past 3 decades, emigration has thrived on Nkoranza's under-development and high unemployment rate. Alle für Artikel : Ghana Lybien Auswanderer Schlagworte für alle : Ghana, Lybien, Libya, Nkoranza, Emigration, Migration, Arbeit, Work, Tripolis
Hoto: DW/Marine Olivesi

Ita ma wannan matar da abun da ta ke cewa, ''Duk abun da ya ce shi ne, ba zai iya tabuka komai ba nan da shekaru hudu, wannan shi ne abun da na ke tsammani.''

Al'umar kasar ta Ghana za ta yi zaman jira na abubuwan da shugaban ya yi alkawarin aiwatarwa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar