1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin shugaban Amirka game da halin da kasar sa ke ciki.

Mohammad Nasiru AwalJanuary 21, 2004
https://p.dw.com/p/BvmQ
Shugaba GWB dai ya yaba da irin managartan ayyukan da yayi a cikin shekaru 3 da ya yi a fadar White House. Shugaban ya ce Amirka ta fuskanci manyan matsaloli a cikin wannan lokaci to amma ta magance su. To sai dai yakin da ake yi da ta´addanci na ci-gaba da zama babban kalubale.

"Yau watanni 28 ke nan tun bayan hare-haren ta´adancin ran 11 ga watan satumban shekara ta 2001, shekaru biyu sun wuce ba tare da an kaiwa kasar mu hari ba. To amma zai zama rashin basira idan muka yi zaton cewa mun kawad da dukkan barazanar da muke fuskanta." Shugaba Bush ya kara da cewa har yanzu ´yan ta´adda na ci-gaba da shirin kai sabbin hare-hare akan Amirka da sauran kasashen duniya. A dangane da haka shugaban ya ce zai ci-gaba da aiki da dokar yaki da ta´addanci a Amirka kana kuma zai ci-gaba da hada kai da sauran kawayen Amirka don yakar ta´addanci a ko-ina cikin duniya. Shugaban ya ba da misali da kasar Libya yana mai cewa saboda sabbin dubarun da ake dauka ya sa kasar ta Libya ta yi watsi da shirye-shiryen ta na kera makaman kare dangi.

"In da ba mu dauki wadannan matakai ba da shugaban mulkin kama karya wato Saddam Hussein ya ci gaba da shirin sa na kera makaman kare dangi. Haka zalika da kudurin MDD bai haifar da wani abin a zo a gani ba, wato kenan da MDD ta yi rauni sannan su kuma ´yan mulkin kama karya sun yi ta cin karensu babu babbaka. Faduwar gwamnatin Saddam Hussein ta taimaka an samu kwanciyar hankali da zaman lafiya a duniya."
Shugaban na Amirka ya yi alkawarin ci-gaba da marawa shirin kafa mulkin demukiradiyya a kasashen Afghanistan da Iraqi. Don ta haka ne kawai wadannan kasashe zasu iya zama misali na kawo canji mai ma´ana a yankunan da suke fama da rikici.
Bush ya sake maimaita aniyar sa ta mika mulki ga ´yan kasar Iraqi a karshen watan yuni. A game da rawar da MDD zata taka a Iraqi kuwa shugaba Bush ya lissafa jerin kasashen da suka tura dakarunsu zuwa Iraqi ne kawai. Sannan a hannu daya ya gargadi masu adawa da manufofin sa game da Iraqi na cikin gida da waje da cewa:

"Tun farkon fari Amirka ta nema kuma ta samu taimakon kasashen duniya game da matakan da ta dauka kann kasashen Afghanistan da Iraqi. To amma da akwai bambamci tsakanin jagorantar wani kawancen kasashen duniya da kuma mika kai ga bukatun wasu tsiraru. Amirka ba zata taba neman izini ba don kare kanta da al´umarta." A game da siyasar cikin gida shugaba Bush ya jawo hankali ne game da bunkasar tattalin arziki da kasar sa ta samu, yana mai ba da misali da karin kayaki da masana´antu ke samarwa da kayan da kasar ke fitarwa ketare da kuma raguwar hauhawar farashin kaya. Ko shakka babu wannan sashe na jawabin shugaban na da muhimmanci a wannan shekara da za´a gudanar da zaben shugaban kasa a Amirka.