Jawabin Shugaba Bush na Amurika a game da kasar Iraki | Labarai | DW | 30.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin Shugaba Bush na Amurika a game da kasar Iraki

Shugaba Bush na Amurika, ya gabatar da jawabi a yammacin yau, a makarantar horra da kurrarun soja, ta Annapolis da ke jihar Mariland a gabancin kasar.

A cikin wannan jawab,i Bush ya bayyana manufofin gwamnati Amurika, a game da kasar Iraki.

Ya ce Amurika a shire ta ke ta ci gaba da girke sojoji a Iraki har lokaci da wannan kasa ta yan ta´adda masu tada zaune tsaeye a dunia.

Yace ba shi da kwankwanto, komin dadewa za a cimma wannan nasara.

Yace burin Amurika shine, na ganin dakarun kasar Iraki ,su da kansu, sun kai ga nasara tsare kasar su ,da kuma hanna yan takife daga ketare su yi anfani da Iraki domin kitsa hare hare ga Amurika.

Jawabin na shugaba Bush, ya sha bambam da littafin da hukumar tsaron kasar Amurika, ta buga, wanda ya bayyana fara janye dakarun kasar daga Iraki, a shekara mai zuwa.

Kamar yada ya saba, Bush ya kekasa kasa, kan cewar babu gudu, babu ja da baya, a game da batun yaki da ta´andancí a Iraki da sauran dunia,muddun ya na matsayin shugaban kasa.