Jawabin shekara-shekara na Georges Bush | Labarai | DW | 24.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin shekara-shekara na Georges Bush

Shugaban Amurika Georges Bush, ya gabatar da jawabi ga al´umma,a game da halin da Amurika ke ciki, ta fannoni daban-daban na rayuwa.

Mahimman batutuwa guda 4 ,da ya ambato, sun haɗa da rikicin Iraki da, harakokin tsaro a cikin Amurika, kazalika George Bush, ya maida hankali a jawabin na sa a kann batun makashi da kuma baƙin haure.

A game da Iraki Bush cewa yayi:

Idan rundunar Amurika, ta hita daga Irak kamin sojojin ƙasar, su samu issashen horo ta fannin tsaro , babu shaka yan takife za su hamɓɓara da gwamnatin Irak.

Za a fuskancin haɗin gwiwa, daga ƙungiyoyin ta´ada iri 3, na farko yan schi´a, masu samun goyan baya daga Iran, sannan yan sunni, masu samun tallafi daga Alqa´ida, sai kuma yan ta´ada masu alaƙa da tsofan shugaban ƙasa.

Tashin hankalin na Irak zai ɓulla a sauran ƙasashen yankin, hakan kuwa ba ƙaramar barazana ba ce ga Amurika.