1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jawabin sabuwar shekara na Angela Merkel

Gräßler, Bernd/SB/AHDecember 31, 2015

Shugabar gwamnatin Jamus ta ambato batun |'yan gudun hijira da na ta'addanci da kuma matsalolin da nahiyar Turai ke fuskana.

https://p.dw.com/p/1HWZJ
Bundeskanzlerin Angela Merkel Neujahrsansprache
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Yayin da aka fara tare da ci gaban tarbar shekara ta 2016 cikin ƙasashen duniya, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga Jamusawa musamman yayin da ƙasar ta karɓi kimanin 'yan gudun hijira milyan ɗaya cikin wannan shekarar da muke mata adabo.

Sakon Angela Merkel zuwa ga al'umma

Kamar yadda aka zata sakon shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel bisa sabuwar shekara ta 2016 mai makawa yana cike da maganganu kan zaman-tare yayin da ƙasar da karɓi kakuncin dubbai ko kuma kimanin 'yan gudun hijira da bakin haure milyan guda.Merkel ta nuna cewar babban abu mai muhimmanci cikin shekara ta 2016 ga al'umar ƙasar na zama aiki tare domin a tinkari matsalar 'yan gudun hijira da suka kwarara zuwa kasar:"Wannan abin da ya zo mana kar mu bari ya kawo mana rarrabuwa. Rarrabuwa tsakanin matasa da tsaffi. Ko tsakanin al'umar da suka ɗaɗe suna rayuwa tare da mu da kuma sabbin zuwa. Kar mu bayar da kafa ga masu nuna kyama da nuna cewar su kadai ne Jamusawa kuma su ne masu ta cewa."

Merkel Neujahrsansprache SPERRFRIST
Hoto: dapd

An yaba da yadda Angela Merkel ta karɓi baƙi a Jamus

Shugabar gwamnatin ta samu yabo a ciki da wajen kasar dangane da matakin da ta daukan kan 'yan gudun hijira da ke kwarara kasar musamman daga wuraren da ake samun tashe-tashen hankula. Amma kuma akwai masu sukar lamarin har ta wasu mambobin jam'iyya mai mulki. Galibi 'yan gudun hijira sun fito daga Siriya inda ake samun tashe-tashen hankula musamman na tsagerun kungiyar IS da ke neman kafa daular Islama.Shugabar gwamnatin Merkel ta kuma yi gargaɗin cewarlamarin 'yan gudun hijira idan aka tafiyar ta hanyar da ta dace ka iya taimakawa bisa zamantakewa na ƙasar.

Neujahrsansprache Angela Merkel 2015
Hoto: Reuters/Maurizio Gambarini