Jawabin Obama kan hukuncin kashe Martin
July 15, 2013Obama ya ce ko da ya ke wannan shari'a ta tayar da hankulan jama'a a Amirka, amma ya zamo wajibi a amince da hukuncin da kotun ta yanke. Shugaban ya kara da cewa ko da yake Amirka kasa ce mai bin doka, to amma akwai ayar tambaya game da hanyar da ta dace a bi domin kawar da sake aukuwar wannan danya. Obama ya fadi haka ne ya na mai nuni da shirinsa na tsananta dokar mallakar makamai.
A watan Fabarairu na shekarar 2012 ne dai George Zimmerman, wanda a wancan lokaci ya ke aikin sa kai na tsaro ya harbe Trayvon Martin a unguwar Sanford da ke jihar Florida. Shi dai Zimmerman mai asali daga Latin Amirka ya ce ya yi hakan ne domin kare kansa. Sai dai masu shigar da kara sun dora masa laifin aikata kisa. Ko shakka babu wannan shari'a za ta janyo tafka muhawara a kan wariyar jinsi a Amirka ..
An dai shirya gudanar da zanga -zanga a duk fadin kasar ta Amirka domin nuna rashin amincewa da hukuncin da kotun ta tyanke na wanke Zimmerman daga laifin aikata kisa.
Mawallafiya. Halima Balaraba Abbas
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe