Jawabin Obama game da Afghanistan | Siyasa | DW | 02.12.2009
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jawabin Obama game da Afghanistan

Ƙasashen dake ƙawance da Amirka, sun yi marhabin lale da jawabin Obama game da ƙasar Afghanistan

default

Shugaban Amurka Barack Obama

A martanin daya mayar dangane da alƙawarin tura ƙarin dakaru dubu 30 zuwa ƙasar Afghanistan da shugaba Obama na Amirka ya yi, sakatare janar na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen, ya ce yana da yaƙinin cewar, sauran ƙasashen dake ƙawance da Amirkar zasu bi sahunta wajen ƙara yawan sojojin da suke dasu a ƙasar ta Afghanistan.

Tuni dai ƙasar Birtaniya ta yi alƙawarin tura ƙarin dakaru 500 zuwa Afghanistan, kana Frime Ministan ƙasar Gordon Brown ya faɗi bayan jawabin Obama cewar, Birtaniya zata ci gaba da taka rawar gani wajen shawo kan sauran ƙasashe su marawa Obama baya wajen aiwatar da sabuwar manufarsa a yaƙin Afghanistan. Itama ƙasar Italiya tace zata ƙara sojojin da bata bayyana adadinsu ba, a yayin da mahukunta a birnin Kabul na Afghanistan ma suka nuna farin cikinsu ga ƙarin dakarun.

Sai dai kuma ya zuwa yanzu ƙasashen Faransa da Jamus, waɗanda ke faɗa a ji a cikin ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO basu kaiga yin alƙawarin tura dakaru ba tukuna. Shugaban Faransa Nikolas Sarkozy, da kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun bayyana cewar, sai bayan wani taron ƙasa da ƙasa akan sha'anin Afghanistan da za'a gudanar ranar ashirin da takwas ga watan Janairu - a birnin London na Birtaniya ne zasu yanke shawara. Sabon Ministan tsaron Jamus, Karl Theodor Zu Guttenberg, ya yi tsokaci game da irin rawar da ƙasarsa zata taka a Afghanistan duk da jawabin na shugaba Obama:

" Ba zamu yi gaggawar amsa kiran da Amirka ta yi mana na tura ƙarin dakaru ba, zamu yi nazari ne sa'annan mu yanke shawarar ko hakan ya dace."

Ministan tsaron ƙasar Denmark Soren Gade, ya ce jawabin Obama na tura ƙarin dakaru - duk da giɓin da kasafin kudin Amirka ke fuskanta wani abin a yaba ne, amma ya ce, Denmark, wadda ke da wakilci a ƙungiyar NATO bata da anniyar tura ƙarin dakaru.

A ƙasar Norway kuwa, Frime Ministan ƙasar Jens Stoltenberg, wanda shima ya yi marhabin da alƙawarin tura ƙarin sojojin da Obama ya yi, ya ce mahukunta birnin Oslo basu da wani shiri na ƙara dakaru akan waɗanda suke dasu yanzu haka a ƙasar Afghanistan. Hakanan batun yake a ƙasashen Australia da New Zealand dake ƙawance da Amirkar, harma da ƙasar Sweden dake riƙe da shugabancin karɓa karɓa a ƙungiyar tarayyar Turai.

Shugaban na Amirka dai, ya ce ya ƙuduri anniyar shawo kan matsalolin da suka hana samun nasara a baya:

" Bayan shekaru takwas na yaƙi a Afghanistan, ina ganin a cikin wasu shekarun - ko dai bamu da isassun kayan aiki ko kuma bamu da ingantacciyar manufa ne yasa bamu kamala aikin ba. Na ƙuduri anniyar kammala wannan aikin."

Sai dai kuma, a yayin da Obama ke da wannan kyakkyawan fata, hatta a safiyar yau larabar nan, rundunar sojin Amirka a Afghanistan, ta sanar da mutuwar wani sojinta, sakamakon ƙawanyar da masu tada ƙayar baya suka yi - lamarin daya kawo adadin sojojin Amirka da suka mutu a Afghanistan zuwa 300 a bana kaɗai.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Hauwa Abubakar Ajeje

 • Kwanan wata 02.12.2009
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/KpBt
 • Kwanan wata 02.12.2009
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/KpBt