Jawabin karba-karba a majalisar Bundesrat | Labarai | DW | 02.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin karba-karba a majalisar Bundesrat

Jam'iyyar the Green a Jamus a karon farko ta gabatar da jawabin karba-karba a babbar majalisar dokokin da ke birnin Berlin

Gwamnan jihar Baden-Wuerttemberg, Winifred Kretschmann shi ne ya jagoranci zaman wanda a yayinsa ya yi magana game da bukatar karfafa 'yancin da daidaikun jihohi ke da shi. Ya ce tabbatar da hakan na da muhimmaci musamman a fannoni ilimi da manyan makarantu da bincike da kuma raya kasa. Gwamnan ya kuma yi kira ga jihohi da su dauki matakin gindaya karin dokoki. Ya ce kashi bakwai daga cikin dari na dokokin kasar ne aka samu daga jihohi. Ya kara da cewa bai dace ba a sakar wa gwmnmati da kuma majalisar dokoki wannan aiki. Shi dai gwamnan jiha da ke jagorantar irin wannan zama shi ne kuma ke wakiltar sauran gwamnoni a duk sanda shugaban gwamnati ya kasa yin aikinsa.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu