1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus:

Mohammad Nasiru Awal AAI
August 30, 2019

Kara tallafi a yankin Sahel mai fama da rikici da kasashen Faransa da Jamus za su yi da kuma harkar man fetur a Kenya da Yuganda da tsadar rayuwa a Zimbabwe ne suka dauki hankali a wannan makon

https://p.dw.com/p/3Olvt
Burkina Faso Ouagadougou | Angela Merkel, Bundeskanzlerin & Treffen G5 Sahel
Shugabannin G-5 Sahel tare da Shugabar Gwamnatin JamusHoto: Reuters/A. Mimault

A wannan makon cikin sharhunan jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka, jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi sharhi mai taken 'karfafa aiki a yankin Sahel' inda ta fara da cewa gwamnatocin Faransa da Jamus za su kara yawan tallafin da suke bai wa yankin mai fama da rikici, sannan sai ta ci gaba tana mai cewa:
A taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki wato G7, kasashen Faransa da Jamus sun amince su karfafa aikinsu a yankin na Sahel. Bayan wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka yi da shugaban Burkina Faso Roch Marc Kabore, kasashen biyu sun ce za su kara yawan kudin da suke bayarwa a aikin samar da tsaro da raya kasa musamman a cikin kasashen nan da suka kulla kawancen G5-Sahel, a kokarin yaki da ta'addanci da magance matsalolin gudun hijira tun daga tushe. Tun 2014 kasashen Mauritaniya da Mali da Niger da Burkina Faso da kuma Chadi suka kafa kungiyar ta G5-Sahel, tun kuma 2017 suke aikin samar da rundunar hadin gwiwar da za ta yaki ta'addanci da sauran manyan laifuka, to amma ana samun tafiyar hawainiya wajen aiwatar da aikin rundunar mai dakaru 5000, duk da alkawura da suka samu daga kasashen ketare.
 
Ita kuwa jaridar Neues Deutschland farawa ta yi da taken 'Harkar man fetur a gabashin Afirka', sannan sai ta kara da cewa karon farko cikin tarihi a farkon wannan mako, kasar Kenya ta fara sayar da man fetur ketare, kasar Yuganda kuma na son ta bi sahu nan da wasu shekaru, amma babu maganar hadin kai. Ta ce a nan gaba gabashin Afirka ka iya zama yanki na biyu mafi girma wajen hakar man fetur a kasashen Afirka na kudu da Sahara sai dai akwai wasu shingaye sakamakon matsaloli na yankin. Jaridar ta ce da farko kasar Yuganda aka fi ganin alamar za ta zama ta farko inda a 2006 a yammacin kasar aka gano rijiyar mai mafi girma a Afirka tun cikin shekaru gommai. Shekaru shida Kenya ta fara aikin neman mai. Sai dai akwai matsala domin a yankin Turkana da ke Arewa maso Yammacin Kenya inda aka gano rijiyar man, an kwashe shekaru gommai da gwamnati a Nairobi ta yi watsi da yankin, yanzu kuma 'yan siyasa a yankin na neman iko da sabbin albarkatun karkashin kasar, abin da ka iya janyo rikici tsakaninsu da kamfanonin mai da kuma gwamnatin tsakiya da ke Nairobi.

Kenia exportiert die erste Lieferung RohölKenia exportiert die erste Lieferung Rohöl
Jirgin fitar da man fetur kasashen wajen daga birnin Nairobi na kasar KenyaHoto: Reuters/J. Okanga
G7-Gipfel in Frankreich Macron und Merkel
Shugabannin Faransa da Jamus a taron G7Hoto: picture-alliance/AP Photo/I. Langsdon
Tag der Arbeit in Harare, Simbabwe
Wani mai kira ga gwamnatin Zimbabwe da ta farka daga bacci kan tsadar rayuwaHoto: AP

Ana fama da karancin kusan komai na kayayyakin masarufi a kasar Zimbabuwe, burodi, man fetur da magunguna sun zama kayan gabas a kasar. Kamar magabacinsa shi ma Shugaba Emmerson Mnangagwa yana daukar matakan ba sani ba sabo kan abokan adawa, inji jaridar Frankfurter Allgemenine Zeitung. Ta ce sama da shekaru guda bayan nasarar lashe zabe da Mnangagwa ya yi, Zimbabuwe na fuskantar barazanar rugujewa. Kasar na fama da matsalar hauhawar farashin kaya. Jaridar ta rawaito wani kiyasi da kungiyoyin agaji suka yi cewa kimanin kashi daya bisa uku na 'yan kasar su miliyan 15 sun dogara kacokan kan taimakon kayan abinci.