1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Ziyarar Netanyahu a gabashin Afirka

Umaru AliyuJuly 8, 2016

Ziyarar Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a gabashin Afirka da shirin Majalisar Dinkin Duniya na kara yawan sojojinta a Mali.

https://p.dw.com/p/1JM1q
Kenia, Benjamin Netanjahu und Uhuru Kenyatta
Benjamin Netanjahu da Uhuru Kenyatta a NairobiHoto: Reuters

Jaridar Tageszeitung ta yi magana game da ziyarar Benjamin Netanyahu na Isra'ila a kasashen Afirka ta Gabas, inda ta ce diplomasiyya da hadin kan yaki da aiyukan tarzoma ne suka mamaye tattaunawa a ziyarar da Firaministan na Isra'ila ya kai Afrika ta Gabas a wannan mako, wadda ita ce ta farko da wani shugaban gwamnatin Isra'la ya kai nahiyar Afirka tsawon shekaru 30. Ya dai fara yada zango ne a Yunda, inda ya yi juyayin cikar shekaru 40 tun da sojojin Isra'la suka kwato 'yan Isra'ila da Falasdinawa 'yan takife suka yi garkuwa da su cikin wani jirgin saman fasinja a birnin Entebbe, ranar hudu ga watan Yuli na shekara ta 1976. Daga baya Netanyahu ya zarce zuwa kasashen Kenya da Ruwanda kafin ya kammala ziyararsa gaba daya a Habasha.

Kara yawan sojojin zaman lafiya a Mali

Mali UN Blauhelmsoldaten
Sojojin kiyaye zaman lafiya a MaliHoto: Getty Images/AFP/H. Kouyate

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta duba aiyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ne a kasar Mali, inda ta ce ko da shike majalisar tana da shirin kara yawan sojojinta a kasar, amma da alamu babu wani abin da zai hana Malin ta ci gaba kan hanyar rushewa da take kai a yanzu. Tsawon shekaru uku kenan rundunar Majalisar Dinkin Duniya wato Minusma, take kokarin kawo zaman lafiya ta hanyar dakatar da aiyukan kungiyoyin jihadin musulunci dabam-dabam da suka mamaye arewacin Mali, amma ya zuwa yanzu ba ta sami nasara ba. Halin da ake ciki, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung bai kai tsananin da za a ce ba zai gyaru ba, amma al'amura suna ci gaba da tabarbarewa a kullum a kasar. Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana da shirin kara yawan sojojinta zuwa adadin 13000, yayin da suma 'yan sandanta da ke kasar za a kara yawansu zuwa 1900.

Tasa keyar 'yan gudun hijira

Deutsch lernen Unterricht Flüchtlinge
Darasin Jamusanci ga 'yan gudun Hijirar Eritriya da ke JamusHoto: picture-alliance/dpa/H. Schmidt

Kasar Sudan tana ci gaba da tura 'yan asalin Eritriya da suka nemi mafaka a kasar zuwa kasarsu ta asali. Wannan dai shi ne bayanin da jaridar Tagesspiegel ta gabatar a wannan mako, inda ta nuna damuwar da gwamnati a Berlin, fadar mulkin Jamus take nunawa a game da abin da zai iya zama makomar 'yan gudun hijiran na Eritriya idan aka maida su tilas zuwa kasarsu. Karamin minista a ma'aikatar harkokin wajen Jamus, Markus Ederer ya ce gwamnatin tarayya tana sane da wannan mataki na Sudan, kuma tana nuna damuwa game da haka, ta kuma shaida wa Sudan cewar wannan abu ne da ko kadan ba mai karbuwa ba ne.

Hukuncin mai sassauci a Afirka ta Kudu

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta duba hukunci mai sassauci da aka zartas kan tsohon sanannen magujin nan na nakasassu dan Afika ta kudu, Oscar Pistorius, inda a tsakiyar mako, alkali Thokozile Masipa a Pretoria ta jefa shi gidan kaso tsawon shekaru shidda saboda laifin kashe budurwarsa Reeva Steenkamp da gangan. Jaridar ta ce wannan hukunci ne da bai taka kara ya karya ba, ganin cewar irin wannan laifi kamata yayi ya dauki hukuncin akalla shekaru 15 a gidan kaso.