Jaridun Jamus: Zimbabuwe da taron Davos sun dau hankali | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 26.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Jaridun Jamus: Zimbabuwe da taron Davos sun dau hankali

Jaridun Jamus a wannan makon sun karkata kan kalaman da shugaban kasar ya yi cewar shi dan kishin kasa a wani jawabi da ya yi a taron Davos kana jaridun sun tabo rikicin siyasar Jamuriyar Demokradiyyar Kwango.

Sabon shugaban Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa ya gabatar da kansa a matsayin dan kishin kasa mai sha'awar farfado da tattalin arziki, amma idan aka yi la'akari da tarihinsa mutum ne da ba za a iya yarda da shi. Jaridar ta ce a jawabin da ya yi a tsakiyar wannan makon a gun babban taro kan tattalin arzikin duniya a Davos Shugaba Mnangagwa ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga masu zuba jari da su saka hannun jari a kasarsa da ya ce yanzu ta bude sabon babi, kofofinta kuma a bude suke ga ‘yan kasuwa. 

Kabila ya murkushe masu bore har yanzu dai jaridar ta Neue Zürcher Zeitung. Ta ce ‘yan sanda a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango sun sake murkushe masu zanga-zangar adawa da Shugaba Joseph Kabila, inda suka kashe mutum shida, suka yi wa 60 rauni sannan suka kame 210 daga cikin masu zanga-zangar da cocin Katholika ya kira a karshen mako. Jaridar ta kara da cewa tun wasu watanni ke nan ake zaman zullumi a Kwango. Tun a watan Disamaban 2016 wa'adin mulkin Kabila ya kare amma sabanin yarjejeniyar da suka kulla da ‘yan adawa har shekarar 2017 ta kare bai shirya sabon zabe ba. 

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung labari ta buga kan wani binciken kayayyakin tarihi tana mai cewa tawagar masana kimiyya da kuma masu nazarin kayayyakin tarihi na jami'ar Abidemi Babatunde Babalola da ke kudu maso yammacin Najeriya da na jami'ar Rice da ke Amirka da suka tono wani birbishin gilashi a garin Igbo Olokun da ke kusa da birnin Ile-Ife sun ce bayan binciken kimiyya da suka gudanar kan gilashi tabbas an sarrafa gilashi ne tsakanin karni na 11 zuwa na 15 shekaru aru-aru gabanin zuwan Turawa gabar tekun yammacin Afirka. Hakan na zama shaida cewa yankin na Kudu maso Yammacin Najeriya ya taba zama ma'aikatar sarrafa gilashi shekaru 600 zuwa 900 da suka gabata.