Jaridun Jamus: Taron kolin AU da rikicin gabashin Kwango | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 03.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Jaridun Jamus: Taron kolin AU da rikicin gabashin Kwango

Taron kolin kasashen kungiyar tarayyar Afirka da sabon rikicin 'yan tawayen kungiyar M23 a Kwango na daga cikin batutuwan Afirka da suka dauki hankalin jaridun na Jamus a wannan makon.

A labarinta mai taken babban jami'an diplomasiyyar nahiyar Afirka jaridar Berliner Zeitung ta fara labarin da cewa karshen tika dai dai tik sanan sai ta ci gaba kamar haka.

Bayan lokacin mai tsawo ana kai komo hade da takaddama tsakanin kasashen Afirka masu magana da harshen Ingilishi da takwarorinsu masu amfani da harshen Faransanci, a karshe dai shugabannin kasashen Afirka 54 sun zabi tsohon ministan harkokin wajen Chadi kuma abokin dasawar Shugaba Idris deby wato Moussa Faki Mahamat a mukamin sabon shugaban hukumar kungiyar AU a taron kolin da suka gudanar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha. Jaridar ta ce Mahamat mai shekaru 56 wanda sai da aka je zagaye bakwai kafin a zabe shi a sabon mukamamin yana da aikin hada kan kasashen Afirka, amma saboda karewarsa a fannin diplomasiyya zai taka rawar gani.

An sake karbar Maroko a cikin AU

Maroko ta koma cikin kungiyar AU inji jaridar Süddeutsche Zeitung a labarin da ta buga game da daya daga cikin batutuwan da suka dauki hankali a taron kolin na kungiyar AU.

Ta ce a 1984 Maroko ta fice daga kungiyar don nuna adawa da goyon bayan da mafi rinjayen kasashen Afirka suka nuna wa yankin Yammacin Sahara da Marokon ta mayar karkashin ikonta. An ba wa yankin da kungiyar Polisario ta ayyanashi da Jamhuriyar Demokradiyyar Sahara matsayin memba a kungiyar. Shekaru 33 baya shugabannin kasashe 39 daga cikin 54 na Afirka sun kada kuri'ar sake shigar da Maroko cikin AU.

Kungiyar 'yan tawayen M23 ta sake kunno kai 

Ita kuwa jaridar die Tageszeitung ta leka yankin gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango tana mai cewa 'yan tawaye da aka yi tsammanin an gama da su sun sake kunno kai a yankin tsanukan gabashin kasar.

'Yan tawayen M23 lokacin da suka karbi iko da garin Goma a shekarun baya

'Yan tawayen M23 lokacin da suka karbi iko da garin Goma a shekarun baya

Ta ce lokacin da jiragen saman alikopta guda biyu na sojojin Kwango suka yi hatsari a kusa da ka iyakar Ruwanda ranar Jumma'a da ta gabata, hankali ya tashi. Ko da yake sojoji sun ce kuskure ya janyo hatsari, amma daga baya 'yan tawayen kungiyar M23 sun yi ikirarin harbo akalla daya daga cikin jiragen saman masu saukar ungulu da ke shawagi a yankin iyakar kasashe uku na Kwango da Ruwanda da kuma Yuganda. An tono gawarwakin matuki da wasu mutane uku da ke cikin jirgi daya, sannan a daya jirgin kuma rauni aka ji daga cikin har da 'yan Rasha su uku da jami'an sojan Kwango su biyu.

Jagoran 'yan demokradiyyar Kwago ya rasu

Etienne Tshisekedi lokacin wani taron jam'iyyar adawa ta UDPS a Brussels a watan Yunin 2016

Etienne Tshisekedi lokacin wani taron jam'iyyar adawa ta UDPS a Brussels a watan Yunin 2016

Har wa yau dai muna a kasar ta Kwango muna kuma tare da jaridar ta die Tageszeitung wadda ta nuna alhini ga rasuwar madugun adawar Kwango Etienne Tshisekedi wanda Alla Ya yi wa rasuwa a birnin Brussels na kasar Beljiyam, inda ya je jinya.

Ta ce ba zato ba tsammani babban jagoran adawar Kwango ya rasu a kasar Beljiyam, daruruwan matasa suka yi jerin gwano suna kukan makoki, daga bisani sun yi cincirindo a gaban gidanshi da ke birnin Kinshasa. A ranar Laraba Tshisekedi da ke zama babban jagoran adawa na tarihi a Kwango ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.