Jaridun Jamus: Taron duniya kan cutar HIV/AIDS | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 22.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Jaridun Jamus: Taron duniya kan cutar HIV/AIDS

Taron kasa da kasa kan cutar AIDS ko Sida da halin da ake ciki a Mali sun dauki hankalin jaridun Jamus a wannan makon.

Jaridar Berliner Zeitung ta fara da cewa babban taron kan cutar AIDS a Afirka ta Kudu ya sanya dogon buri, inda aka kuduri aniyar kawo karshen annobar kwayoyin HIV kafin shekarar 2030. Jaridar ta ce kwararrun masana a fannin binciken kimiyya da masu fafatuka da kuma wakilan gwamnatoci sun kwashe tsawon kwanaki biyar suna tattaunawa kan kudurin gamaiyar kasa da kasa na kawo karshen yaduwar HIV a duniya baki daya nan da shekaru 14 masu zuwa. Jaridar ta kara da cewa ko da yake an samu gagarumin ci-gaba a yaki da cutar musamman a bangaren magungunan rage kaifin kwayoyin HIV amma har yanzu da akwai bukatar cigaba da wayarwa da mutanen kai game da cutar.

Dangantakar auren dole da cutar AIDS

Ita kuwa a labarinta game da cutar ta AIDS jaridar Neues Deutchland cewa ta yi rashin makoma bayan aure tana mai nuni da yadda 'yan matan da iyayensu ke yi musu auren dole, ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar. Ta ce an jima ana watsi da alakar da ke akwai tsakanin aurar da yara kanana da barazanar kamuwa da kwayoyin HIV. Sakamakon wani bincike na Hukumar yaki da AIDS ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi ya nuna yawan 'yan mata fiye da kima da ke kamuwa da cutar. Kashi biyu bisa uku na sabbin wadanda suka harbi da kwayoyin HIV 'yan mata ne ko matasa mata 'yan shekaru 10 zuwa 24.

Halin rashin tabbas a tsakiyar Mali

Mali Unruhen Polizei

Duk da sintirin da jami'an tsaro ke yi har yanzu ba a samu zaman lafiya mai dorewa a Mali ba

A wannan makon jaridar Die Tageszeitung ta leka kasar Mali ne inda ta yi sharhi game da wani hari da aka kai kan wani barikin soji da ya yi sanadin rayuka 17, lamarin da ta ce ya fito da rashin kwanciyar hankali a tsakiyar kasar ta Mali.

Ta ce: Baya ga sojoji 17 da suka rasa rayukansu a harin da wasu mahara dauke da manyan makamai suka kai a kan barikin Nampala da ke kan iyakar Mali da kasar Mauritaniya, inda kuma ba su fuskanci wata turjiya ta azo a gani ba, sun kuma raunata mutane sama da 30. Yanzu an shiga cikin rudu, domin harin ya nuna irin mawuyacin halin da rundunar sojojin Mali ke ciki shekaru hudu bayan tawayen Abzinawa, da rikicin kasa da mamayen masu kaifin kishin addini a arewacin kasar, da kuma girke sojojin duniya a yankin.

Maroko ta kuduri aniyar komawa cikin dangin AU

Marokko König Mohammed VI in Rabat

Sarki Mohammed na hudu

Kasar Maroko na son ta sake komawa cikin kungiyar Tarayyar Afirka inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, inda ta kara da cewa kamfanin dillancin labarun Maroko ya rawaito cewar Sarki Mohammed na hudu ya aike wa shugaban kungiyar AU Idris Deby wannan niyya a lokacin taron kolin shugabannin Afirka na baya bayan nan da ya gudana a birnin Kigalin kasar Ruwanda. Mahaifin Basaraken wato Sarki Hassan na biyu ya janye wakilcin kasar daga kungiyar a 1984, don nuna adawarsa da shigar da yankin Yammacin Sahara cikin OAU.