1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus sun leka Kwango da Ruwanda

Abdullahi Tanko Bala
January 4, 2019

Jaridun Jamus na wannan mako sun duba batun katse sadarwa intanet a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a lokacin zabe da na hana shigo da gwanjo a Ruwanda

https://p.dw.com/p/3B2yc
Ruanda Radio "Izamba"
Hoto: DW/E. Topona

Za mu fara sharhin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. A sharhinta mai taken gwagwarmayar sauyin Dimukuradiyya. Jaridar ta ce kwana guda bayan zaben kasa a Kwango, shugaban kasar Joseph Kabila ya kassara harkokin sadarwar Internet. Tun daga ranar Litinin aka toshe dukkan kafofin sada zamunta da hanyoyin internet a manyan biranen kasar. 


Ministan sadarwa na kasar ya tabbatar da daukar matakin ba tare da yin wani karin haske ba. Koda a baya ma dai gwamnatin ta taba toshe kafofin internet domin hana 'yan adawa shirya zanga-zanga. Dan takarar adawa Martin Fayulu ya ce matakin ya nuna karara yunkurin gwamnati na yi musu kwace game da nasarar da suka samu a zaben da ake fata a karon farko za a mika mulki daga gwamnatin farar hula zuwa wata cikin lumana da kwanciyar hankali. 


A kasar ta Kongo da ta sha fama da yaki, zaben ya gudana ba tare da tashin hankali ba. Shugaban kasar dai Joseph Kabila ya ce bai fidda tsammanin sake komawa fagen siyasa ba bayan shekaru biyar lamarin da ya kara jaddada shakkun cewa dan takarar da yake mara wa baya Eammnuel Ramazini Shadary na zama dan kore a gare shi. Ita kuwa jaridar BildPlus ta rubuta sharhinta ne a kan yawon cirani da 'yan Afirka ke yi zuwa Turai.


Jaridar ta ruwaito shugabar kasar Habasha Sahle-work Zewde a wata ganawa da ta yi da Shugaban Gwamnatin Ostriya Sebastian Kurz. Ta ce Afirka ba ta jin dadin yadda matasa ke fadawa hadari a yunkurinsu na zuwa Turai, ta ce sai bango ya tsage kadangare ke samun wajen fakewa. Idan da kasashen Turan ba su bude kofarsu ba da jama'a ba za su kwarara ta hanyoyi masu hadari zuwa kasashen ba. Jaridar ta ce magance matsalolin Afirka tun daga tushe shi ne mafi a'ala da kuma samun makoma mai kyau. Sai dai ta yi tambayar shin nahiyar Turai za ta rufe idonta ga matsalolin talauci da yake-yake da kan sa jama'a yin kaura daga Afirka? 

 

54. Münchner Sicherheitskonferenz MSC 2018 Paul Kagame
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Gebert

Ruwanda ta haramta shigar da kayan gwanjo cikin kasarta, amma shin za ta iya kauce wa manufar hadewar duniya wuri daya, wato globalisation? Wannan  shi ne sharhin da jaridar Die Zeit ta rubuta.


Gwamnatin Ruwandar na kokari ne domin karfafa kamfanoni da masakunta na cikin gida kuma ba za su iya dorewa ba a karkashin halin da ake ciki na shigo da tsoffin kayan gwanjo daga waje. A hannu daya dai ana iya cewa gwamnatin na kalubalantar manufar nan ta bai daya wato globalization. Shin kananan kasashe makomarsu na hannun kasashe ne 'yan jari hujja? ko kuwa akwai wata hanyar da kasa kamar Ruwanda za ta iya cire wa kanta kitse a wuta?.


Shawarar haramta shigar da tsoffin kaya daga waje abu ne da ya dade kuma Ruwanda ba ita ce ta fara daukar wannan mataki ba. A shekarar 2015 kasashe da dama na gabashin Afirka sun yanke irin wannan hukunci daga 2019 sun haramta shigar da gwanjo cikin kasashensu. A daya hannun kungiyar dillalan tufafi ta Amirka, matakin bai yi mata dadi ba, domin masaku da yawa na Amirka za su rasa aiki. A kan haka Shugaban Amirka Donald Trump ya matsa wa kasashen Kenya da Uganda da kuma Tanzaniya su yi wa Allah da Annabinsa su bar wannan maganar. Ruwanda ce kadai ta saura wadda ta nuna turjiya.


Shugaban Ruwandan Paul Kagame ya fada a baya cewa shan koko bukatar rai, kin sa kayan gwanjo magana ce ta kare kima da martaba, ba za mu sa kayan da wasu suka cire suka yar ba. Sannan kuma muma so mu karfafa masakunmu wadanda za su iya samar wa mutane dubu 25 aiki. Koda a bara ma dai kasar ta Ruwanda ta kaddamar da wani shiri da ta yi wa take "Made in Rwanda" wato kayan da aka yi a Ruwanda domin karfafa wa kananan masana'antu da 'yan kasuwa na cikin gida. Sai dai wasu na ganin cewa wannan batu ne kawai na siyasa kuma gwamnatin na da wata manufa.