1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus sun dubi zabuka a wasu kasashen Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 10, 2018

https://p.dw.com/p/32yTu
Mali Wahlen
Hoto: Imago/Le Pictorium/N. Remene

Za mu fara sharhunan na yau da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta ce Kabila ya dauki irin matakin da Putin ya dauka. Ta ce shugaban kasar Kwango Joseph Kabila ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar ba, sai dai wani hanzari ba gudu ba ana iya cewa har yanzu ba ta sake zani ba, domin akwai yiwuwar Shugaba Kabilan ne zai ci gaba da mulki.

Wannan dai shi ne karo na farko da aka ji labari mai dadi daga Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon bayan tsahon watanni na rashin tabbas. Kabila ba zai tsaya takara ba. Tsawon lokaci, Kabila da ke da shekaru 47 a duniya da ke mulkin kasar tun daga shekara ta 2001 ya dauka ba tare da ya ce uffan ba kan sake tsayawa takara a zaben da za a gudanar a watan Disamba mai zuwa. A ranar Laraba sa'o'i kalilan gabanin rufe rajistar tsayawa takara ga hukumar zaben kasar ta KWango. A karshe Kablia ya bara, inda ya bayyana Emmanuel Ramazani Shadary a matsayin wanda zai gaje shi. 

DRC Präsident Joseph Kabila
Hoto: Reuters/K.Katombe

Jaridar ta ce, 'yan takara 26 ne dai za su fafata a zaben na watan Disamba, sai dai kadan daga cikinsu ne ke da damar lashe zaben. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna dan takarar jam'iyyar adawa Moise Katumbi da ke gudun hijira a kasar Beljiyam kuma tsohon gwamnan gundumar Katanga, na kan gaba. Sai dai Katumbi bai samu damar yin rijistar takararsa ba, bayan da mahukuntan Kwangon suka hana shi damar shiga kasar. Mutum na biyu da ake tsammanin zai iya lashe zaben bayan Katumbi, shi ne Jean-Pierre Bemba, wanda ya dawo daga kotun duniya mai hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa-da-kasa da ke birnin Hague bayan wanke shi da aka yi daga zargin aikata laifukan yaki a watan Yunin da ya gabata.

Mali Wahlen - Ibrahim Boubacar Keita
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Ita kuwa jaridar die tageszeitung ta yi nata sharhin mai taken zagaye na biyu a zaben Mali cewa ta yi: Jagoran adawa Soumaïla Cissé da ke da shekaru 68 a duniya zai fafata da Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta mai lakanin (IBK) a zagaye na biyu na zaben Mali da zai gudana ranar a wannan Lahadin 12 ga watan Agustan da muke ciki. Cissé dai ya samu sama da kaso 17 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zagaye na farko na zaben da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata. A nasa bangaren Ibrahim Boubacar Keita, ya samu sama da kaso 41 cikin 100 na kuri'un, wanda hakan ke nunin cewa jam'iyya mai mulki ta samu kasa da kaso takwas cikin 100 ne na kuri'un kacal. Duk da cewa masu sanya idanu a zaben zagayen farkon sun yaba da yadda ya gudana, da dama daga cikin 'yan adawa na ganin an tafka magudi. Wasu kuma sun ce sun ga ana raba kudi a wasu kauyuka a jajiberin zaben, sai dai babu tabbas  kan wadannan zarge-zargen.

Simbabwe Wahl | Nelson Chamisa, Opposition - MDC
Hoto: Reuters/P. Bulawayo


Jaridar Süddeutsche Zeitung kuwa ta rubuta sharhinta ne mai taken sabon taku da sauyin da bai taka kara ya karya ba. Jaridar ta ce bayan bayan nasara mai cike da rudani da Shugaba Emmerson Mnangagwa ya samu a Zimbabuwe, kasar ta fada cikin yanayi na rudani, su kansu 'yan adawar sun zamo ba abin yarda ba. Bayan ayyana sakamakon zabe a Zimbabuwe, birnin Harare ya zamto tamkar babu wanda ya lashe zaben. Babu bukuwa ko murna, mutane sun shiga ayyukansu na yau da kullum, rana ce da ta kasance tamkar wadanda suka fadi zabe ne kawai a kasar. Tun da fari hukumar zaben kasar ta jinkirta sanar da sakamakon zaben shugaban kasa.

Ana iya cewa mahukuntan sun yi haka ne domin dakile duk wata dama ta yin zanga-zanga, sai dai hakan bai yiwuwa ba, an gudanar da zanga-zangar abin takaici hakan na faruwa kusan ko yaushe a kasashen Afirka. Da kaso sama da 50, Shugaba Emmerson Mnangagwa ya lashe zaben, yayin da dan takarar jam'iyyar adawa ta MDC Nelson Chamisa ya sami kaso 44 cikin 100 na kuri'un da aka kada kamar yadda hukumar zaben kasar ta bayyana, sakamakon da 'yan adawar suka ce ba su amince da shi ba. ))