Jaridun Jamus: Murkushe boren ′yan adawa a Habasha | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 12.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Jaridun Jamus: Murkushe boren 'yan adawa a Habasha

Matakan ba sani ba sabo kan zanga-zangar 'yan adawa a Habasha da halin tsaro a Mali da harkar tsoffin tufafi a Afirka.

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus game da nahiyar ta Afirka da jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka kasar Habasha wato Ethiopia tana mai cewa:

Bisa ga dukkan alamu murkushe zanga-zangar 'yan adawa a karshen makon jiya a Ethiopia ya janyo asarar rayuka fiye da alkalumman da suka fito fili. Jaridar ta ce kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ruwaito shaidun ganin ido na cewa akalla rayuka 97 suka salwanta sannan daruruwa suka jikkata. Wani jami'in diplomasiyya shi ma ya tabbatar da mutuwar mutane 47. Sai dai masu lura da al'amuran yau da kullum sun ce yawan rayukan da aka rasa na da yawan gaske kasancewa lamarin ya auku ne a wurare da dama da labarai ke da wahalar fita waje.

Samar da cibiyar jigilar dakarun duniya a Mali

Shirin Jamus na samar da wata cibiyar kasa da kasa da za ta kula da jigilar kayayyaki da kuma dakarun kasa da kasa a Mali ya tsaya cik, inji jaridar Franfurter Allgemeine Zeitung.

Ursula von der Leyen in Mali Tieman Hubert Coulibaly

Ursula von der Leyen a wata ziyara da ta kai Mali

Jaridar ta ce shekara daya da rabi ke nan da kulla yarjejeniya tsakanin ma'aikatar tsaron Jamus da kamfanin kera jirgin sama na Airbus don samar da jiragen saman yaki masu saukar ungulu da na jigilar kayayyaki da marasa lafiya da za a yi amfani da su a yankuna masu fama da rikici, inda kuma aka girke sojojin kasa da kasa, amma har yanzu wannan shiri da ministan tsaron Jamus Ursula von der Leyen ta bada sanarwar aiwatar da shi, bai kankama ba. Yanzu haka dai ministar ta ce mai yiwuwa sai a karshen lokacin bazara ne jiragen saman na alikofta daga Jamus, za a iya amfani da su a kasar Mali, musamman ga sojojin rundunar Minusma don kare sojojin da ke sintiri a kasa.

Cinikin tsofaffin tufafi ko gwanjo a Afirka

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung a wannan makon ta duba harkar cinikin tsofaffin tufafi ne wato kayan gwanjo da ta ce su ne ke kassara masaku da sauran kamfanonin samar da tufafi a Afirka, amma duk da haka an samu guraben aiki yi sakamakon harkar ta tsofaffin tufaffi musamman daga kasashen Turai da Amirka.

Afrika Kenia Altkleider

Kasuwar kayan gwanjo a kasar Kenya

Ta ce da zarar wadannan hajojin sun isa Afirka sai su tashi daga matsayin kayayyakin tallafi. Ta ce harka da tsofaffin tufafin yanzu ta zama babban kasuwanci, abinda masu sukar lamiri suka ce shi ya hana masu samar da tufaffi na cikin gida a kasashe masu tasowa damar tsayawa da kafafunsu ko ma suka durkushe gaba daya, ya kuma lalata guraben aiki. Wannan dai shi ne zargin da aka rika yi musamman a shekaru gommai na 1990, amma yanzu kamar yadda jaridar ta Berliner Zeitung ta nunar, ko su kansu masana tattalin arzikin na da ra'ayi dabam dangane da tsofaffin tufafin daga Turai. Ta ce baya ga araharsu ta yadda masu karamin karfi a Afirka ke iya saya, sun fi sababbin tufafi masu araha daga nahiyar Asiya inganci da kwari.