Jaridun Jamus: Kungiyar AU ta kasa daukar mataki kan rikicin Burundi | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 05.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Jaridun Jamus: Kungiyar AU ta kasa daukar mataki kan rikicin Burundi

AU ta yi watsi da shirin aikewa da dakarun zaman lafiya kasar Burundi mai fama da rikici, amma za ta mika batun ga Majalisar Dinkin Duniya.

Za mu sharhin jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta yi tsokaci kan taron kolin kungiyar tarayyar Afirka AU da ya gudana a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Ta ce a kowace shekara kungiyar na zaban sabon shugaba, a wannan karon shugaban Chadi Idris Deby ya karbi ragamar shugabancin kungiyar. A jawabinsa shugaba Deby ya ce dole ne kasashen Afirka su magance matsalolinsu da kansu, inda ya kara da cewa a kullum suna taro, suna yawan surutai da rubuce-rubuce da yawa, amma matakan da suke dauka kadan ne, a wasu lokuta ma ba sa tsinana komai. Hakika a taron kolin na bana AU ta yi watsi da shirin aikewa da dakarun zaman lafiya zuwa kasar Burundi mai fama da rikici. Ta ce za ta mika batun ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya.

Hada karfi don yakar tarzoma a yankin tafkin Chadi

Tallafin kudi don yaki da Boko Haram inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung.

Ta ce bisa ga dukkan alamu yanzu an samu kudin kafa rundunar kasa da kasa ta Afirka da za ta yaki Boko Haram a Najeriya da kasashe makwabta. Jaridar ta rawaito jami'an diplomasiyyar Afirka da na Turai a birnin Addis Ababa shalkwatar kungiyar tarayyar Afirka na cewa adadin kudin da aka alkawarta bayarwa ya kai dala miliyan 250. An yi hasashen ware wa rundunar mai yawan sojoji 8700, dalar Amirka miliyan 110 a shekara, wanda mafi yawa zai fito daga Najeriya, ita kuma tarayyar Turai za ta taimaka da dala miliyan 50. Sojojin sun fito ne daga kasashen Najeriya, Chadi, Kamaru, Nijar da kuma Benin.

Matsalar 'yan awaren Biafra a Najeriya

'Yan aware sun yi garkuwa da wani jirgin ruwa a gabar tekun Najeriya inji jaridar Neue Zürcher Zeitung a labarin da ta buga da ke mayar da hankali kan matsalar Biafra.

Ta ce 'yan aware da ke neman 'yancin kan Biafra a Najeriya sun yi garkuwa da wani jirgin ruwan dakon man fetir na kasar Girika, kuma sun yi barazanar tarwatsa jirgin da bam hade da ma'aikatansa 'yan kasashen waje muddin mahukunta a Najeriya ba su sako jagoransu Nnamdi Kanu ba. Jaridar ta ce wannan lamarin ya yi tuni da yakin Biafra na kusan shekaru 50 da suka wuce. Ta ce rahotanni ma sun nuna cewa 'yan awaren na Biafra na hada karfi da sojojin sa kai na yankin Niger Delta da suka yi suna wajen kai hari kan bututun man fetir. Wannan halin da ake ciki na zama wani karin matsin lamba ga gwamnatin Najeriya da ke yakar kungiyar Boko Haram a arewacin kasar.

Yunwa sakamakon fari a wasu yankunan Afirka

A labarin da ta buga mai taken yunwa ta dawo jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce matsalar fari mafi muni cikin shekaru ta afka wa kasashen Habasha da Malawi da Mosambik da kuma Afirka ta Kudu. Yanzu haka dai miliyoyin mutane a wadannan kasashe sun dogara kan taimakon abinci. Jaridar ta ce wannan halin ya nuna rashin tabbas ga bunkasar tattalin arziki da ake samu a wasu kasashen najiyar ta Afirka.