1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta dauki hankulan jaridun Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 30, 2018

Zafafan hare-hare a Najeriya sun dauki hankulan jaridun Jamus na wannan makon, sun yi nazari kan hare-hare mafi muni da kungiyar ta kai tun bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya dare karagar mulki a shekara ta 2015.

https://p.dw.com/p/39DUo
Nigeria Präsident Muhammadu Buhari bei Militär in Maiduguri
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta wallafa labari mai taken zafafan hare-hare a Najeriya. Jaridar ta ce kungiyar 'yan ta'adda ta zafafa hare-harenta a Najeriya. Ta ce wannan ne hare-hare mafi muni da kungiyar masu kaifin kishin addnin suka kai a Najeriya tun bayan darewar shugaban kasar Muhammadu Buhari kan karagar mulki a shekara ta 2015.

Jaridar ta ci gaba da cewa, a cikin mako guda 'yan ta'addan IS reshen yammacin Afirka ta hallaka mutane 118 a Najeriya, ciki har da sojoji sama da 100. Wannan kisan dai ya bayyana ne cikin wani faifen bidiyo da kungiyar ta fitar. Kungiyar ta fara ne da kai hari a ranar 16 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki kan sansanin sojoji da ke kauyen Kareto, inda ta hallaka kimanin sojoji uku yayin da wasu da ba a san adadinsua ba suka yi batan dabo. Jim kadan kuma suka sace wasu mata bakwai a garin Bama da ke jihar Borno, kafin cikin dare kuma su kai hari kauyen Mammanti inda suka hallaka mutane tare da yin gaba da daruruwan shanu. Daga bisani sojoji sun dakile harin ta hanyar kai musu farmaki da jiragen sama.
 

Sharhi kan salon mulkin Shugaba Magufuli

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta sharhinta ne kan sabon shugaban kasar Tanzaniya John Magafuli mai taken, ''Daga shugaban kasa mai kawo sauyi zuwa dan kama-karya''. Jaridar ta ce shugaban kasar Tanzaniya John Magufuli ya samu lakani wanda ya yi dai-dai da shi tsahon shekaru. Sunan ya dace da shi a yayin da ya ke matsayin ministan ayyuka a Tanzaniya, haka kuma sunan ya dace da shi lokacin da kwatsam ya zamo shugaban kasar a shekara ta 2015 kana abin koyi ga kasashen Afirka. A yanzu ma da magoya bayan Magufuli suka fara yi masa kallon sabon shugaban mulkin kama karya sunan nasa wato: "tingatinga", ma'ana Trakta ko kuma motar rushe gine-gine Bulldozer, sunan ya dace da shi.

John Magufuli Präsident Tansania
Hoto: picture-alliance/AA/B. E. Gurun

Shekaru ukun da suka gabata, Magufuli ya fara da abin arziki ta hanyar kokarin yakar almundahana da kudaden al'umma da kuma tsuke bakin aljihu domin samo wa kasarsa mafita. Ya kori manyan jami'an gwamnati da suke amfani da mukaminsu ta hanyoyin da ba su dace ba tare da zaftare rabin majalisar zartaswarasa domin biyan albashin ma'aikata. Sai dai mai shekaru 59 a duniya Magaufuli ba wai kawai masu almundahana da kudaden al'umma yake kamawa ba har ma da masu adawa da shi. Tuni kasashen Turai suka fara juya masa baya, inda yake kokarin samun sababbin abokan hulda, hakan ce ma ta sanya ya sake karfafa dangantaka da China.

Illar guguwa ga kasar Somaliland


Bari mu karkare da jaridar Berliner Zeitung da ta rubuta sharhinta ne a kan matsalar talauci da yunwa a yankin Somaliland. Jaridar ta ce yankin Somaliland da ke nahiyar Afirka yana da kyau da kuma talauci. Mazauna yankin na fafutukar yakar yunwa tun daga shekara ta 1991, yayin da gwamnatin ke fafutukar ganin duniya ta san da ita da kuma kokarin daidata al'amura. Watanni kalilan da suka gabata, guguwa ta lalata komai. An yi asarar rayuka da dukiyoyi.

Somaliland Wahlen
Hoto: Getty Images/AFP