Jaridun Jamus: Harin Ouagadougou da rikicin Kwango sun dau hankali | Zamantakewa | DW | 09.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Jaridun Jamus: Harin Ouagadougou da rikicin Kwango sun dau hankali

Harin ta'addancin da ya girgiza babban birni kasar Burkina Faso a ranar Jumma'a ta makon jiya ya dauki hankalin jaridun Jamus

A labarin da ta buga a kan batun jaridar Neue Zürcher Zeitung ta fara ne da cewa rashin tabbas a Burkina Faso bayan harin da aka kai a birnin Ouagadougou hankali ya karkata kan alaka tsakanin 'yan ta'addar da sojojin kasar da kuma wani janar da aka zarga da yunkurin juyin mulki. Jaridar ta ce kungiyar jihadi ta GSIM da ke zama reshen kungiyar Al-Kaida ta dauki alhakin harin daya a hedkwatar soji daya kuma kusa da ofishin jakadancin Faransa, ya hallaka sojoji takwas da maharan su takwas sannan wasu 80 suka jikkata. Amma bisa la'akari da yadda aka tsara kai harin a kan hedkwatar sojojin kasar da kayan sarki da 'yan ta'adda suka yi amfani da su, akwai kyakkyawan zaton cewa 'yan ta'addar sun san ciki da wajen hedkwatar watakila suna da alaka da sojoji. Mahukunta da ke gudanar da bincike na kyautata cewa akwai hannun manyan jami'an sojojin kasar a ciki.

Kasar Mali na a cikin jerin kasashen da rundunar sojojin Jamus za ta kara yawan sojojinta a ciki inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai mayar da hankali kan matakin da gwamnatin tarayyar Jamus ta dauka na tura karin sojojinta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a ketare.
Ta ce za a kara yawan sojojin Jamus da ke aiki karkashin inuwar rundunar Majalisar Dinkin Duniya a Malin wato Minusma da sojoji 100 wato yawansu zai tashi daga 1000 a yanzu zuwa 1100. An dauki wannan mataki ne don karfafa aikin sojojin na Jamus a kasar ta Mali da har yanzu ke fama da hare-haren masu kishin addini. Sai dai babban dalilin da ya sa aka kara yawansu shi ne yanzu rundunar ta Bundeswehr ce ta karbi jagorancin sansanin sojoji da ke garin Gao, inda aka girke mafi yaan sojojin na Jamus. Bugu da kari saboda yadda makamai da kayan aikin sojojin ke saurin lalace saboda yanayin zafi na yankin Hamada, to akwai bukatar kara yawan masu tura kaya da makanikai a yankin.

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon labari ta buga dangane da rikici a lardin Ituri na kasar Jamhuriyar Dempkaradiyyar Kwango tana mai cewa, a kullum ana kai hare-hare kan kauyukan kabilar Hema da ke a lardin na Ituri, lamarin da ya tilasta mutane dubu 250 tserewa zuwa tudun mun tsira yayin da wasu kimanin dubu 42 suka samu mafaka a kasar Yuganda. Jaridar ta ce wannan shi ne sakamakon tashe-tashen hankula na baya bayan nan da suka addabi lardin da ke Arewa maso Gabashin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango, amma har yanzu gwamnati ba ta dauki wani mataki na kawo karshen rigingimun ba.

A karse sai kasar Afirka ta Kudu inda jaridar Berliner Zeitung ta ruwaito cewa mutane 180 aka tabbatar sun rasa rayukansu sakamakon cin abinci da nau'in nama da suka harbu da wata kwayar cuta da ake wa lakabi da Listeria. Masana sun ce wannan shi ne lamar i mafi muni dangane da barkewar cutar Listeria a tarihin dan Adam, inda a cikin shekara guda ta yi sanadi na rayukan mutum 180 cikii har da yara 78. Jaridar an dauki tsawon shekara guda kafin a shawo kan annobar.