1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon malamin jami'a ya zama shugaban Somaliya

Zainab Mohammed Abubakar ZUD
May 20, 2022

Jaridun Jamus sun yi sharhi kan sabon shugabancin Somaliya da yadda ambaliyar ruwa ta tagayyara Afirka ta Kudu tare da aniyar Amirka ta sake tura sojoji Somaliya.

https://p.dw.com/p/4BdPO
Somalia Präsident Hassan Sheikh Mohamud
Hoto: Farah Abdi Warsameh/AP/picture alliance

A cikin makon nan ne Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta wallafa labari mai taken "Sabon Shugaban Somaliya yana da mayakan kishin Islama da fari a matsayin manyan abokan gaba". Jaridar ta ci gaba da cewa, Hassan Sheikh Mohamud ya taba zama shugaban kasar a baya, don haka al'ummar Somaliya na da kyakkyawar fata a kan sa.

Wani abu da sabon shugaban ba zai iya cewa ba, shi ne na bai san irin kalubalen da ke gabanshi ba. Hassan Sheikh Mohamud ya fara rike mukamin shugaban Somaliya ne tun daga shekarar 2012 zuwa 2017, kasar da ke yankin kuriyar Afirka, wadda dama ke cewa tana fama da rikice-rikice da zai hana a ayyanata  a matsayin kasa.

A ranar Lahadin da ta gaba ne dai aka sake zaben Mohamud a matsayin shugaban Somaliya. A yanzu haka yana mulkin kasar da mutane miliyan shida ke fuskantar yunwa, inda masu tada kayar baya da ke kawance da kungiyar al-Qaida ke iko da yankuna da dama, inda kuma 'yan siyasarsa suka kusan jefa kasar cikin wani sabon yakin basasa a bara.

Somalia Hassan Sheikh Mohamud
Hoto: Abukar Mohamed Muhudin/AA/picture alliance

Mai shekaru 66 da haihuwa Hassan Sheikh Mohamud ya kasance mashawarcin Majalisar Dinkin Duniya kuma mai fafutukar zaman lafiya kuma shugaban jami'a kafin ya fada siyasa gadan gadan a matsayin shugaban jam'iyya a 2011. Shekara daya kacal bayan nan, majalisar wakilai ta zabe shi a matsayin shugaban kasa. Zargin cin hanci da rashawa ya mamaye wa’adin mulkinsa da ya gabata. Wani rahoto na Majalisar Dinkin Duniya a 2013 ya nuna cewa, masu mukami na  gwamnati na kallon Babban Bankin Somaliya tamkar wurin ajiyarsu.

Duk da haka, zaben da aka yi a baya-bayan nan na Mohamud ya samu kyakkyawan martani. Na farko, kasancewar shi ne karo na hudu da aka mika mulki cikin lumana a Somaliya tun daga shekara ta 2000. Na biyu, saboda da yawa sun dauki Mohamud a matsayin mai sulhuntawa fiye da wanda ya gabace shi.

Ambaliyar ruwa ta jikkata Afirka ta Kudu

Südafrika Überschwemmungen nach Unwettern
Hoto: RAJESH JANTILAL/AFP

Ita kuwa jaridar die Tageszeitung sharhi ta yi game da tattalin arziki da muhalli mai taken "Ambaliyar ruwa a Afirka ta Kudu". Ta ci gaba da cewa, yana daya daga cikin bala'o'i mafi girma da suka afku a Afirka ta Kudu a tarihinta. A gabar tekun gabashin kasar, ruwan sama ya yi kamari na tsawon kwanaki a cikin watan Afrilu wanda daga karshe ruwa ya mamaye sassan kasar. 

Ambaliyar ta yi sanadiyyar rayukan sama da mutane 450, a yayin da ta lalata dubban gidaje da sauran halittu, kana ta tilasta rufe tashar jiragen ruwa ta Durban, birni mai yawan mutane sama da miliyan daya na wucin gadi. 

A cewar die Tageszeitung, idan aka yi nazari da kyau, ba bala’i ne daga indallahi kawai ba, har ma da sakaci na dan Adam. A yanzu dai ta tabbata cewa sauyin yanayi, wanda ke da nasaba da hayaki mai guba da masana'antu ke fitarwa ka iya zama musabbabin annoabr. Wannan shi ne sakamakon binciken masana kimiyya daga shirin bincike na yanayin duniya. A cewar binciken, dumamar yanayi ta ninka ruwan sama mai yawa har sau biyu. 

Amirka za ta sake kai sojoji Somaliya

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta buga wani labari mai taken "Me ya sa Biden ke sake tura sojojin Amurka zuwa Somaliya?". Shugaban Amirka Joe Biden ya amince da sake tura sojojin Amirka zuwa kasar Somaliya da ke fama da yakin basasa na tsawon lokaci.

Buffalo I Biden kritisiert  Ideologie von Rechten
Hoto: Scott Olson/AFP/Getty Images

Jaridar ta ce Biden ya bi bukatar ma’aikatar tsaron Amirka ta Pentagon, wadda ke son a girke dakarun kasar na musamman 500 a Somaliya, domin fuskantar barazanar da mayakan sa-kai na al-Shabaab ke yi. Da wannan mataki, Biden ya sauya matakin da magabacin sa, Donald Trump, ya dauka, wanda ba zato ba tsammani ya janye sojojin Amirka 750 daga Somaliya a makonnin karshe na gwamnatinsa.

Kafofin yada labaran Amirka sun ambato wata babbar majiyar gwamnati na cewa za a yi amfani da wadannan sojoji  ne wajen kalubalantar kungiyar al-Shabaab. Sojojin na Amirka ba rundunonin fada ba ne, a cewar Washington, amma an yi nufin su zama masu horarwa, masu bayar da kayan aiki da kuma masu bayar da shawara don horar da sojojin Somaliyan da zummar yaki da al-Shabaab.