1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jaridun Jamus: Dakatar da zabe a Mali

Abdullahi Tanko Bala
September 29, 2023

Dage shirin gudanar da zabe a Mali wanda sojojin da mulkin kasar suka yi da kuma janyewar Faransa daga kasar Nijar na daga cikin batutuwan da suka dauki hankali jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/4WyGe
Hoto: AP Photo/picture alliance

Bari mu yaye kallabin shirin da jaridar Die tageszeitung wadda ta buga labari mai taken " Sojojin Mali sun dakatar da shirin zabe". Jaridar ta ce, ya kasance sirri mafi muni a Mali. Ba za a gudanar da zaben da za a kawo karshen mulkin soja a kan lokaci ba.

Jadawalin gwamnatin mulkin sojan na Mali kan zaben ya fara ne daga zabukan ‘yan majalisar dokoki a ranar 29 ga Oktoba 2023 zuwa zaben shugaban kasa a ranar 4 ga Fabrairu, 2024. Da yammacin ranar litinin aka fitar da sanarwar gwamnati da ke soke zaben ‘yan majalisar dokokin kasar tare da dage na shugaban kasa, saboda abun da aka danganta da dalilai na fasaha.

Mali I Referendum
Hoto: Sia Kambou/AFP/Getty Images

Wannan ba abin mamaki ba ne, tunda babu alamun shirye-shiryen zabe duk da cewar sun ce an dage ne na gajeren lokaci. Babu 'yan takara ko yakin neman zabe, kuma babu wurin rajistar masu zabe a halin yanzu. 

Akwai dalilai da dama da za su iya sa a dage zaben, tun daga dage zaben, zuwa karuwar tashe-tashen hankula a sassan kasar. Sai dai wannan ba shi ne dalilin da ministan da ke da alhakin gudanar da zaben Abdoulaye Maiga ya bayar ba, ya ce ba a sabunta rajistar masu zabe ba saboda kamfanin da aka bai wa alhakin gudanar da rajistar na kulle.

Karin Bayani:Rigingimu sun dabaibaye zaben kasar Mali

"Faransa ta janye daga yankin Sahel" taken labarin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta wallafa kenan kan kai ruwa rana tsakanin Faransa da Nijar da ta nemi raba gari da uwargijiyarta a baya. Jaridar ta ce, bayan juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar, Shugaba Emmanuel Macron ya sanar da janye sojojin Faransa daga wannan kasa ta Sahel.

Mali Frankreich beendet die Operation „Barkhane“
Hoto: AP Photo/picture alliance

Ana iya cewar Faransa na fuskantar wani mummunan yanayi a duniyar da take taka rawarta yadda take so tsawon shekaru ko bayan zamanin mulkin mallaka a kasashen na yammacin Afirka, kamar yadda Faransawa ke kiran yankin a matsayin nasu inda siyasarta ke tasiri. Watanni biyu bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar ta janye jakadanta da kuma sojoji 1,500 daga kasar.

A wata hira da yayi da wasu kafofin yada labaran Faransa, Shugaba Emmanuel Macron ya nuna damuwa matuka game da halin da yankin ke ciki, kasancewar Faransa ce a wasu lokuta da kanta ta dauki alhakin yaki da ta'addanci na masu tsattsauran ra'ayi a yankin, don haka ne ma yake matukar alfahari da sojojin. Amma yanzu za su yada kwallon mangwaro su huta da kuda.

'Yan gudun hijira a Tunisiya
'Yan gudun hijira a TunisiyaHoto: Hasan Mirad/Zumapress/picture alliance

A ranar 26 ga watan Yuli ne dai Nijar ta bi sahun Mali da Burkina Faso na kasancewa karkashin mulkin soji, kuma nan take matsayin Faransa ya canza. Nijar din da ke zama kasa ta karshe a shiyyar ta sauya matsayi daga aminiya zuwa abokiyar gaba. Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Janar Abdourahamane Tiani ya ayyana Faransa a matsayin makiya tare da yin kira ga Paris da ta janye jakadanta daga Yamai.

Za mu karkare da labarin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta wallafa mai taken" Kowa yana so ya fice daga Tunisiya". Jaridar ta ce 'yan ci-rani na cigaba da fuskantar matsin lamba a kokarinsu na shiga Turai don samun tudun mun tsira. Fiye da bakin haure 5,000 ne suka isa Lampedusa a ranar 12 ga watan Satumba kadai, adadin da ya shige na kowane lokaci cikin tsukin sao'i 24.

Turai dai ta damu matuka dangane da yadda 'yan gudun hijirar ke son barin Tunisiya. Masana sun danganta kokarin barin kasar da 'yan cirani ke yi saboda yanayi na kyama da suke fuskanta daga mahukuntan kasar.