1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona ta rage yawan tashe-tashen hankula a wasu kasashe

Mohammad Nasiru Awal
May 2, 2020

Dokar kulle da aka kafa a wasu kasashen Afirka don dakile yaduwar Corona ta rage yawan aikata laifuka sai dai ana kira ga manyan kasashe da su tallafawa kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/3bhE3
Coronavirus Südafrika Johannesburg Essensausgabe
Hoto: AFP/L. Sola

Za mu fara sharhi da labaran jaridun Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta leka kasar Afirka ta Kudu tana mai cewa haramcin sayar da barasa ya canja kasar Afirka ta Kudu. Ta ce tun lokacin da aka sanya dokar kulle aka kuma haramta sayar da barasa, tashe-tashen hankula da fashi da makami da ma yawan kisan kai sun ragu a kasar. Sai dai jaridar ta ce yanzu 'yan kasar sun koma dafa giya ta gargajiya inda suke amfani da abarba ko citta ko masara. Afirka ta Kudu dai na daga cikin kasashen duniya da aka fi shan barasa, inda alkalumma suka nuna cewa a kowace rana kowane dan kasar kan sha kwalaba guda ta barasa abin da ya ninka sau uku yawan wadda ake sha a Jamus. Da yawa daga cikin 'yan kasar na cewa corona ta sa sun koma bin al'adunsu na gargajiya da suka gada kaka da kakanni, musamman bangaren sarrafa giya a gargajiyance. Sai dai jaridar ta ce ana iya komawa gidan jiya da zarar an soke dokar kulle aka kuma dage haramcin sayar da barasa a kasar.

Tallafa wa tattalin arzikin kasashen Afirka saboda corona

Nigeria Abuja | Coronavirus | Jack Ma Hilfsgüter
Sauke kayan agaji na magunguna da Chaina ta ba wa NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Tsarin sauyi ga Afirka wannan shi ne taken labarin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta buga, inda ta kara da cewa annobar Covid-19 ta jefa da yawa daga cikin kasashen Afirka cikin matsalar tattalin arziki, saboda haka ana bukatar sauyin tunani na taimakon da ake ba wa nahiyar. Abin da ya kamata manyan kasashen duniya irin su Jamus su yi, shi ne hulda da kasashen nahiyar ta Afirka tsakani da Allah ba da kuma nuna girman kai ba. Jaridar ta ce ko da yake annobar ta shafi duniya gaba daya, amma kasashe masu karfin tattalin arziki na da nauyi kansu na inganta huldodin kasuwanci da na zuba jari da takwarorinsu kasashe masu tasowa, don a gudu tare a tsira tare. Jaridar ta kara da cewa bayan annobar, bai kamata nahiyar Turai  ta mayar da hankali kanta kadai ba, wajibi ne ta kuma duba makomar tattalin arzikin nahiyar Afirka gaba daya.

Sauyi ga matakan yin kaura zuwa Turai

Libyen | Rettungsschiff Alan Kurdi» nimmt Migranten auf
Sau tari bakin haure kan bi hanyoyi masu hatsari ciki har da ta kan teku don shigowa TuraiHoto: picture-alliance/dpa/Cedric Fettouche

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon ta ruwaito wasu shawarwari ne da kwararrun masana kan kaura a Jamus suka mika wa gwamnatin tarayyar Jamus na neman a yi sauye-sauye a dokokin yin kaura don ba da damar yin kaura ta halal daga Afirka zuwa Turai. Masanan suka ce masu bi ta barauniyar hanya mai kuma hatsari zuwa Turai kan ba wa masu fataucin mutane dubban kudi na Euro, maimakon haka duk mai son zuwa Turan yana iya ajiye wadannan kudade a matsayin garanti ko jingina a ofisoshin Turai da ke kasashensu, su kuma su ba shi bisar shigowa Turai ya yi aiki na gajeren lokaci ya koma gida ya kuma karbi kudin jinginar. Ba a dai sani ba ko mahukuntan Turan za su amince da wannan shawara.