1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Wani kusan kungiyar anti-Balaka ya shiga hannun kotu

Zainab Mohammed Abubakar AMA
March 18, 2022

Batun gurfanar da tsohon shugaban kungiyar anti-Balaka a gaban kotun duniya mai hukunta manyan laifukan yaki da cutar Coronavirus a Afirka, sun ja hankalin jaridun Jamus a wannan mako.

https://p.dw.com/p/48gqr
Zentralafrikanische Republik Anti-Balaka Miliz
Hoto: Reuters/B. Ratner

Za mu fara da jaridar die Tageszeitung wadda ta ce daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya zuwa kotun duniya da ke birnin the Hague. Jaridar ta bayyana yadda aka kama tsohon jagoran 'yan tawaye na kungiyar anti-Balaka, Maxime Makon, mai matsanancin ra'ayin addinin Kirista, wanda aka bi da shi ta kasar Chadi kafin zarcewa zuwa kasar Netherlands inda zai fuskanci tuhuma kan abin da ya aikata a kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula.

Tun shekara ta 2018 kotun duniya mai hukunta manyan laifukan yaki ke neman Makom, wanda cikekken sunansa shi ne Maxime Jeoffroy Eli Mokom Gawaka, bisa laifukan da ya aikata tsakanin shekara ta 2013 da 2014, lokacin da kungiyar ta Anti-Balaka ta masu kishin addinin Kirista ta aikata laifuka kan tsurarun Musulmai na kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Ita dai anti-Balaka ta kasance martani ga kungiyar Seleka ta Musulmai, wadda ta kwace madafun ikon kasar daga hannun tsohon Shugaba François Bozize.

Turai tana bukatar nahiyar Afirka

Belgien Brüssel | EU-Afrika-Gipfel | Ursula von der Leyen und Macky Sall
Ursula von der Leyen da Macky Sall Hoto: John Thys/AFP/Getty Images

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi sharhi mai cewa, mayar da hankali kan tashe-tashen hankula da ake a nahiyar ta hanyar aiki tare. Jaridar ta ce lokaci da dama ana ganin banbanci hulda tsakanin Turai da Afirka, kamar yadda aka gani lokacin annobar cutar coronavirus gami da kwararan 'yan gudun hijira daga nahiyar da ke neman kai wa ga tudun mun tsira a kasashen Turai. Kuma lokaci ya yi na aiwatar da shirin kashe kudi kimanin Euro-milyan dubu-150 kan inganta kayayyakin more rayuwa a nahiyar Afirka, kamar yadda aka cimma tsakanin wakilan kungiyar kasashen Tarayyar Turai da na Tarayyar Afirka. Jaridar ta ce nahiyar Afirka tana da matukar tasiri ba ga Turai kadai ba, har da China da Rasha da suke ci gaba da zawarcin samun karin ingizo a nahiyar ta Afirka.

Riga-kafi mai yawa, amma kariya kadan a Afirka

Ana ta bangaren Süddeutsche Zeitung ta yi sharhinta da ke cewa bayan mahawa ta tsawon lokaci kasashen Amirka da na Turai gami da Indiya da Afirka ta Kudu sun amince da sassauta dokokin mallaka kan riga-kafin cutar coronavirus, domin kamfanonin hada magunguna na kasashe masu tasowa su samu damar samar da riga-kafin cikin sauki. Amma Tarayyar Turai tana jiran amincewa daga mambobin kasashen.

Ngozi Okonjo-Iweala | nigerianische Politikerin
Shugabar (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala Hoto: Martial Trezzini/KEYSTONE/picture alliance

Ngozi Okonjo-Iweala shugabar kungiyar kasuwanci ta duniya (WTO) ta ce matakin gagarumin ci-gaba nebayan shafe lokaci ana kulla yarjejeniyar mai wahala. Kasashe masu karfin tattalin arziki sun yi riga kafin har ga yara 'yan makaranta, yayin da manyan ake matakin na karfafa riga-kafin cutar ta coronavirus. Yayin da kasashe masu tasowa suke gwagwarmayar samun riga-kafin. Amirka ta ba da goyon ga shirin na samar da riga-kafin sannan ta matsa lamba ga kasashen Turai suka amince da matakin da zai taimaka kasashe masu tasowa su samu riga-kafin cikin sauki.