1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Inganta muhalli ta sauya makamashi a Japan

Suleiman Babayo AS
October 26, 2020

Firaminista Yoshihide Suga na Japan ya ce gwamnati ta dauki gagarumin matakin kare muhalli cikin shekaru 30 masu zuwa nan da shekara ta 2050 zuwa makamashi da babu iska mai guba.

https://p.dw.com/p/3kSJ8
UN-Generaldebatte Yoshihide Suga
Hoto: UNTV/AP/dpa/picture-alliance

Firaminista Yoshihide Suga na kasar Japan ya kaiyade lokaci zuwa shekara ta 2050 za ta daina fitar da iska mai gurbata muhalli da ke nuna irin burin da kasar ta saka a gaba na inganta makamashi da dakile matsalar saukin yanayi.

Firamnistan ya fadi haka lokacin da yake gabatar da manufofin gwamnati a gaban majalisar dokoki a karon farko tun lokacin da ya dauki madafun ikon kasar wadda ke matsayi na uku wajen karfin tattalin arziki tsakanin kasashen duniya.

Tuni masu rajin kare muhalli da majalisar Dinkin Duniya suka yaba da matakin mahukuntan na Japan waken mika wuya ga muradun kare muhalli a duniya.