1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Japan ta gano gurbatacciyar rigakafin COVID-19

August 26, 2021

Ma'aikatar Lafiya ta kasar Japan ta dakatar da yi wa 'yan kasarta rigakafin corona samfurin Moderna. Japan dai ta dogara ne kaco-kan a kan kamfanin Moderna wurin samar mata da rigakafi.

https://p.dw.com/p/3zWi7
Japan US Premierminister Yoshihide Suga
Hoto: Sadayuki Goto/AP/picture alliance

Hukumomin sun ce sun dauki matakin ne bayan wasu gurbatattun alluran rigakafin da suka gano. Hakan kuma ya sanya Japan jingine kimanin allurai sama da miliyan daya da rabi da ake zullumin sun gurbata.

To amma kamfanin na Moderna da kuma hukumomin kasar sun ce hakan bai shafi ingancin rigakafin ba, sun dakatar da bayar da ita ne domin kariya a kan abin da amfani da gurbatattun rigakafin ka iya haddasawa. Kamfanin ya ce shi ma daga bangarensa ya kaddamar da bincike a kan lamarin.

Firaministan Japan Yoshihide Suga ya ce wannan tsaiko ba zai kawo musu koma baya a kokarinsu na ba 'yan kasar kariya daga coronavirus ba.