1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Japan: Shekaru 72 da harin Amirka a Hiroshima

Salissou Boukari MNA
August 6, 2017

A wannan Lahadin ce kasar Japan ke tunawa da zagayowar cikon shekaru 72 da jefo ma ta bam na farko na nukiliya a birnin Hiroshima da ke kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/2hlbd
Hiroshima Erinnerung an Atombombenabwurf vor 72 Jahren
Japan na tunawa da shekaru 72 da sako bam a HiroshimaHoto: Picture-alliance/AP Photo/R. Ozawa

A ranar 06 ga watan Agusta na shekarar 1945 da misalin karfe 08 da mintuna 15 agogon kasar ta Japan wani jirgin yakin kasar Amirka ya sako bam din na farko, sannan bayan kwanaki uku Amirkar ta sake sako wani bam na biyu na nukiliya a birnin Nagasaki wanda hakan ya sa Japan ta bada kai bori ya hau a ranar 15 ga watan na Augusta  kwanaki shida baya, wanda ya kawo karshen yakin duniya na biyu.

Firaminista Shinzo Abe na Japan da ke magana a dandalin zaman lafiya na Hiroshima, ya ce kasar Japan za ta ci gaba da kokowa ta yaki da kaurace wa makaman nukiliya a duniya.

"Daga nan Hiroshima ina mai jaddada kira ga kasashen da ke da makaman nukiliya, da kuma wadanda ba su da shi, fatanmu shi ne na hada kan bangarorin biyu don samun duniya wadda babu makaman nukiliya a cikinta."

Bam din dai na farko ya haddasa mutuwar mutane dubu 140 a Hiroshima yayin da na biyun ya hallaka mutane dubu 74 birnin Nagasaki