1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Gobara a Japan ta hallaka mutane da dama

December 17, 2021

Wata gobarar da ta tashi a safiyar wannan Juma'ar a birnin Osaka na kasar Japan kana  ta yi kusan mintuna 30 tana ci, ta yi sanadiyyar rasuwar mutane 28.

https://p.dw.com/p/44PFh
Japan Brand in Osaka
Hoto: Kyodo News/AP Photo/picture alliance

Kimanin mutane 27 ne ake fargabar sun mutu a sanadiyyar wata gobara da ta tashi a wani gidan haya mai bene takwas a birnin Osaka na kasar Japan.

'Yan sandan kasar sun ce sun kaddamar da bincike don gano musabbabin tashin gobarar. Kafar yada labaran Japan ta NHK ta nuna yadda hayaki ke fitowa daga tagogin benen da lamarin ya faru. 

Bayan mutane 27 da suka hadu da ajalinsu hukumomi sun ce akwai mutum guda da ya tsira da rayuwarsa duk da munanan raunukan da ya samu.