Afirka ta kudu ta kai matakin karshe a gasar zari-ruga
October 28, 2019Wannan zai bai wa Springbox ta Afirka ta Kudu damar haduwa da Ingila a wasan karshe biyo bayan nasarar da Ingila ta samu inda ta doke mai rike da kambun zarin ruga na duniya New Zealand da ci 19 da 7 a wasan da aka kara a ranar Asabar.
Wannan dai zai kasance maimancin abin da ya faru a gasar Zari ruga ta duniya da Faransa ta dauki bakwanci a shekara ta 2007 wacce Afirka ta Kufdu ta lashe a gaban Ingila duk da danganta babbar kungiyar All Blacks ta Ingila da manyan dawa na fagen zari ruga na duniya. Sai dai Keftain din kungiyar zari ruga ta Afirka ta Kudu Siya Kolisi ya ce, salon tafiyar da al'amura na sabon mai horaswa Rassie Erasmus ya kai su ga wannan nasarar.
"Ya bani kwantiragi lokacin da nake da shekaru 18 kawai, saboda haka na sanshi sosai saboda ya horas da 'yan wasa da dama. Ya nakalcemu, saboda haka ne ya hada kawunanmu domin mu amince da tsarinshi. Tun lokacin da ya iso ya bayyana cewar kungiyar Sping Box ta fi komai muhimmanci a gareshi, alahli a baya kowa daga cikinmu na yi gaban kansa don yin suna ta hanyar amfani da kafofin sada zumunta na zamani. Sai dai ya jawo hankali domin mu yi wasa bil hakki da gaskiya, duk sauran abubuwan za su samu hannu a hankali."
Ranar Jumma'a mai zuwa za a kara wasan neman matsayi na uku a gasar ta zari-ruga ta duniya tsakanin New Zealand da Wales. Sannan a ranar Asabar da ke tafe za a kara wasan karshe domin sanin kasar za ta zama zakara ta duniya tsakanin Ingila da ake sa wa rai da kuma Afirka ta Kudu.Sai dai kowace daga cikin kungiyoyin na neman lashe kofin duniya na zari ruga a karo na uku.