Janye dakarun Chadi daga Jamhuriyar Nijar | BATUTUWA | DW | 13.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Janye dakarun Chadi daga Jamhuriyar Nijar

An fara samun martani bisa matakin kasar Chadi na janye daruruwan sojoji daga kasar Jamhuriyar Nijar wadanda suke aikin bisa tabbatar da tsaro sakamakon rikicin Boko Haram.

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da fara janye dakarun kasar Chadi daga Jamhuriyar Nijar wadanda suke aikin samar da tsaro sakamakaon rikicin Boko Haram da ya ritsa da wasu kasashe na Afirka wadanda suka hada da Najeriya, da Jamhuriyar Nijar, da Kamaru gami da Jamhuriyar Nijar.

Ana sa ran amfani da sojojin na Chadi wajen karfafa tsaro musamman kan iyakar kasar ta Chadi da kuma Libiya, inda ake samun matsaloli na tsaro gami da masu safarar mutane masu neman shiga kasashen Turai. Hukumomin na Jamhuriyar Nijar sun ce tun watanni shida da suka gabata aka fara matakin na yanje sojojin Chadi musamman daga yankin Diffa wanda ya gamu da hare-haren tsageru masu nasaba da Boko Haram.

Sauti da bidiyo akan labarin