1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bankwana da gwarzo Muhammad Ali

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 11, 2016

Dubun-dubatar mutane ne suka halarci jana'izar fitaccen jarumin wasan dambe na duniya dan kasar Amirka da ya rasu a ranar Jumma'a uku ga wannan wata na Yuni da muke ciki, wato Muhammad Ali.

https://p.dw.com/p/1J4ks
Bankwana da Muhammad Ali cikin alhini
Bankwana da Muhammad Ali cikin alhiniHoto: Reuters/C. Barria

An dai gudanar da jana'izar ta Muhammad Ali ne a mahaifarsa da ke birnin Kentucky na kasar Amirka, inda mashahuran mutane da dama suka samu halarata tare da yin jawabai. A jawabin da ta yi, mai dakinsa Lonnie Ali ta bayyana alhininta tana mai cewa:

"Ya na son mu yi amfani da rayuwarsa da mutuwarsa a matsayin wani babban darasi ga matasa da yara masu tasowa da kasarsa da ma duniya baki daya. Yana son mu tunatar da mutane da ke cikin halin kaka nika yi cewa, shima ya fuskanci rashin adalci tun ya na karami, bai samu sakewar da zai yi abin da yake so ba."

Muhammad Ali ya rasu bayan ya sha fama da rashin lafiya yana da shekaru 74 a duniya ya kuma bar mace guda da 'ya'ya tara.