Janaízar Boris Yelsin | Labarai | DW | 25.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Janaízar Boris Yelsin

A yau a birnin Mosco zaá yi janaízar Marigayi tsohon shugaban kasar Rasha Boris Yeltsin. Mahukunta a kasar ta Rasha sun kebe yau a matsayin ranar makoki a fadin kasar domin nuna alhini ga mamacin. Ana sa ran shugabani daga sassan kasashe na duniya da suka hada da tsohon shugaban Amurka Bill Clinton da George Bush babba da kuma shugaban kasar Jamus Horst Köhler za su halarci janaízar. Tun da farko dubban jamaá sun yi bankwana da mamacin inda aka ajiye gawar sa a cocin Christ the Saviour a birnin Mosco. Boris Yelsin ya zamo shugaban kasar Rasha na farko da aka zaba bisa tafarkin dimokradiya a shekarar 1991, ya kuma yi shekaru takwas a kan karagar mulki kafin ya yi murabus a shekarar 1999. Yayin ya kasance wanda ya dora kasar Rasha kan tafarkin dimokradiya dana tattalin arziki, shine kuma wanda ya fara kaddamar da yaki a kan musulmi yan awaren Chechnya wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban jamaá. Ya rasu a ranar litinin da ta wuce sakamakon bugun zuciya.