Jan aikin da ke gaba a yaki da Ebola | Labarai | DW | 02.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jan aikin da ke gaba a yaki da Ebola

Kwamiti na musamman da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa kan yaki da cutar Ebola ya ce ko kusa bai kai ga shawo kan bazuwar cutar da irin ta'adin da ta ke yi ba.

Shugaban kwamitin Anthony Banbury wanda wa'adin da aka deba masa don yin aiki ya kawo karshe ya ce akwai jan aiki a gaba wajen kawar da annobar sai dai ya ce kwamitin nasu a kwanaki 90 din da aka deba musu ya yi bakin iyawarsa wajen sauke nauyin da aka aza masa.

To amma Mr. Banbury din ya ce ya na da yakinin cewa duniya za ta iya kawar da cutar baki daya daga nan zuwa karshen shekarar da muke ciki sai dai fa ya ce akwai jan aiki a gaba a cikin watannin da ke tafe.