Jamusawa sun sami hadari a gasar Rio de Janeiro | Labarai | DW | 12.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamusawa sun sami hadari a gasar Rio de Janeiro

Shugaban tawagar 'yan wasan kwale-kwalen na Jamus Michael Vesper ya ce daya daga cikin 'yan wasan nasu ya samu mummunan rauni.

Die deutschen Kanuten Christian Bahmann und Michael Senft bei den Racing World Championships in Penrith, Australien

'Yan wasan kwale-kwale daga Jamus

Wasu ma'aikata a tawagar wasannin tsere da kwale-kwale daga Jamus da ke halartar wasannin Olympics a kasar Brazil sun sami mummunan hadari kamar yadda jami'ai suka bayyana a ranar Juma'an nan.Shugaban tawagar 'yan wasan kwale-kwalen na Jamus Michael Vesper ya ce daya daga cikin 'yan wasan nasu ya samu mummunan rauni. Ya ce suna ci gaba da tattaunawa da Dokta Bernd Wolfarth da ke zama likitan da ke jan ragamar tawagar 'yan wasan daga Jamus.

Babu dai karin bayanai game da halin da 'yan wasan ke ciki kawowa yanzu daga tawagar ta Jamusawa. Sai dai mai magana da yawun kwamitin shirya wasannin na Olympics Mario Andrade ya ce ya ga mutane biyu daya daga cikin jagoran tawagar 'yan wasan kwale-kwale daga Jamus na komawa masauki a cikin motar haya da tasi.