Jamusawa 8 sun mutun a harin Istanbul | Labarai | DW | 12.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamusawa 8 sun mutun a harin Istanbul

Rahotanni daga kasar Turkiya na cewa akalla mutane 8 daga cikin goma da suka rasu a cikin harin kunar bakin waken da aka kai a cibiyar kasuwancin kasar ya yi sanadiyar mutuwar baki masu yawon bude ido

Firaministan kasar ta Turkiya Ahmet Davutoglu ne ya tabbatar wa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel hakan a tattaunawarsu ta wayar tarho.

Firaministan kasar ta Turkiya dai, ko baya ga mika gaisuwar ta'aziyya ga shugabar gwamnatin Jamus, ya kuma tabbatar mata da gabatar mata da illhirin sakamakon binciken da za su gudanar, dama bayar da kulawa ga Jamusawan da suka jikkata.

Alkaluman baya-bayan nan sun bayyana mutuwar mutane 10 da jikkatar wasu 15 a cikin harin kunar bakin waken da aka kai a safiyar wannan Talata a filin Sultanahmet na birnin Istanbul,harin da tuni hukumomin kasar Turkiyar suka dora alhakin kai shi ga kungiyar IS.