1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iftila'i: Jamus za ta tura tawaga Lebanon

August 5, 2020

Jamus ta sanar da cewa za ta tura wata tawaga mai mutane 47 zuwa  kasar Lebanon bayan wata fashewar wani abu da aka samu a ranar Talata kusa da tashar jirgin ruwan Beirut.

https://p.dw.com/p/3gS7Y
Libanon Explosion in Beirut
Hoto: Getty Images/AFP

Kawo yanzu fashewar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 100 yayin da dubbai kuma suka jikkata. 

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta ce lamarin ya lalata mata ofishin jakadancinta na Lebanon. A sakamakon haka tawagar kwararrun ta Jamus za ta je Beirut domin taimaka wa mahukuntan kasar ci gaba da ceto rayukan wadanda lamarin ya shafa. 

Wannan na zuwa ne a yayin da Faransa ta sanar da cewa a ranar Alhamis Shugaba Emmanuel Macron zai je Lebanon domin jajanta wa mahukuntan kasar da kuma bayar da taimakon da ya dace.