1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin tsuke bakin aljihu a Jamus

Sadissou YahouzaJune 7, 2010

A wani mataki na riga kafin kariyar tattalin arziki, gwamnatin Jamus ta ƙuduri aniyar tsuke bakin aljihu

https://p.dw.com/p/Nk1X
Angela Merkel na bayyani game da wajibcin tsuke bakin aljihuHoto: AP

Gwamnatin Jamus ta shiga kwana na biyu kuma ƙarshe a tattanawar da take  game da fasalin kuɗin da ya tanadi tsuke bakin aljihun gwamnati.A jiya Lahadi, mahalarta taron sun cimma matsaya ɗaya, game da matakai da dama na wannan kasafi.

Burin da fadar mulkin birnin Berlin ke buƙatar cimma, shine rage giɓin kuɗaɗen gwamnati, a matsayin wani mataki na riga kafi ga faɗawa cikin matsalar tattalin arziki da ta fara ɓulla a wasu ƙasashen Turai.

To saidai jam´iyar adawa ta SPD ta bakin kakakinta  Olaf Scholz wamnnan mataki bai dace ba:

" Ba ƙaramin haɗari ne ba, gwamnatin za ta saka al´umma a ciki.Wannan mataki ya sha bamban da alƙawarin da suka yi, lokacin yaƙin neman zaɓe."

Hasashen da masana al´ammuran kuɗi suka yi,ya hango cewar Jamus zata yi tsimin aƙalla Euro miliyan dubu 51 nan da shekara ta 2016.Kuma mafi yawan kuɗin da za a rage sun shafi sashen tallafi ga iyalai marassa ƙarfi. 

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Halima Balaraba Abbas