Jamus za ta tallafawa Mali | Labarai | DW | 21.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta tallafawa Mali

Shugabannin kasashen Turai sun yi alkawarin agazawa kasar don kakkabe 'yan ta'dda musamman bayan harin Bamako inda ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya nunar cewar har yanzu da sauran jan aiki a Mali

Har kawo yanzu hukumomin kasar Mali na ci gaba da neman wadanda suke tuhuma da alhakin hari kan kasaitaccen otel a birnin Bamako. A harin dai kimanin mutane 19 suka mutu, aka sari 'yan kasashen waje. Yanzu haka dai kasashen duniya sun tashi wajen tallafawa Mali bisa yakar ta'addanci. Inda misali ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayannan karin hummasan da Jamus za ta yi a Mali. Inda ministan ya kara da cewa "Wannan harin alama ce da ke nuna har yanzu kasar Mali na a cikin halin rashin tabbas, tana kuma bukatar taimakon gamaiyar kasa da kasa. Muna ba da ta mu gudunmawa karakshin Tarayyar Turai da kuma MDD. Za mu fadada goyon baya da taimakon da muke bayarwa."