Jamus za ta taimaka wa dakarun Afirka da kayan aiki | Labarai | DW | 23.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta taimaka wa dakarun Afirka da kayan aiki

A ganawar da ta yi da shugaban AU Boni Yayi a Berlin, Angela Merkel ta ce sojojin Jamus ba za su shiga yakin da ake da nufin kwato arewacin Mali daga masu kishin addini ba.

A yakin da ake yi da 'yan tawayen Islama a Mali, Jamus za ta taimaka da jiragen saman daukar kaya da ba da horo ga sojojin Mali da kuma kayan aiki ga dakarun kasashen Afirka. An jiyo hakan ne daga bakin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel bayan ta gana da shugaban kungiyar tarayyar Afirka Thomas Boni Yayi a birnin Berlin. Sai dai ta ce Jamus ba za ta aike da sojojinta kasar ta Mali ba.

"Jamus ba ta tunanin tura sojoji duk da cewa Faransa ta yi kira da mu gaggauta yin haka. Na fada wa shugaban cewa su yi kokari don ganin dakarun ECOWAS sun karbi jan ragamar aikin tabbatar da tsaro a Mali daga sojojin Faransa."

Aikin sojojin Jamus a Mali dai shi ne na jigilar dakarun Afirka a babban birnin Mali wato Bamako, mai tazarar daruruwan kilomita daga filin daga.

Shi kuwa a nasa bangaren shugaban AU kuma shugaban kasar Benin Thomas Boni Yayi ya ce kasancewar sojojin Faransa a Mali ba ta da nasaba da wata manufa ta mulkin mallaka, illa wata dama ce ta tabbatar da 'yancin walwala.

"Na gaya mata cewa na yi rangadin nahiyar Afirka gaba daya kuma dukkan shugabannin kasashen nahiyar sun nuna jin dadin irin namijin kokarin da Faransa ta nuna na gaggauta tsoma baki a rikicin."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe