1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron gwamnoni a Jamus

January 19, 2021

Jamus na duba hanyoyin daga wa'adin dokar kulle bisa la'akari da alkalumman masu kamuwa da Corona a kasar.

https://p.dw.com/p/3o6mL
Deutschland Berlin Angela Merkel
Hoto: John MacDougall/AP/picture alliance

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel gami da gwamnonin jihohin kasar  goma sha shida ne ake sa ran za su sake zama a ranar Talatar nan, domin duba hanyoyin kara tsaurarawa da ma tsawita dokar kulle har sai illa masha Allahu.

Da alama dai za a kara tsawaita dokar da ke kawo karshen wa'adinta 31 ga wannan watan na Janiaru, wadda kuma ta haramta bude shaguna da makarantu da ma wuraren shakatawa da wasanni.

Ga alamu tsawaita dokar dai ba za ta rasa nasaba da yawan masu kamuwa da cutar ba da ake kara samu, bayan da a ranar Alhamis da ta gabata kasar ta samu mutane sama da 1,240 na wadanda suka mutu a rana guda, alkalumma mafi yawa tun bayan bullar cutar a Jamus