Jamus za ta kara tsaro a bikin al'adun gargajiya na Carnival | Labarai | DW | 10.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta kara tsaro a bikin al'adun gargajiya na Carnival

Arnold Plickert shugaban kungiyar 'yan sandan GDP da ke jihar da ke a Yammacin Jamus ya ce ba za a lamunci wani hali ba na rashin da'a.

Karneval 2015 Schull und Veedelszöch

Yara 'yan makaranta a lokacin bikin al'adu na Carnival a Köln

Cin zarafin mata da aka yi a birnin Köln na kasar Jamus a jajiberin sabuwar shekaran nan abin da ake zargin mutane daga Arewacin Afirka musamman Larabawa cikin 'yan gaba-gaba da sa hannu a ciki, wata alama ce da ke nuna cewa dole a kara tsaurara matakan tsaro a lokutan bukukuwean al'adu na Carnival da za a yi a wata mai zuwa a biranen da ke gefen kogin Rhine a cewar jami'an 'yan sanda.

Arnold Plickert shugaban kungiyar 'yan sandan GDP da ke jihar da ke a Yammacin Jamus ya ce ba za a lamunci wani hali ba na rashin da'a daga kowane rukunin al'umma, ganin irin abin da ya faru a wannan lokaci da ake shiga sabuwar shekara wanda koda a jiya Asabar sai da jami'an 'yan sanda suka yi dagaske wajen hana rikidewar zanga-zangar adawa da cin zarafin matan da aka yi a birnin dan kada ta zama tashin hankali.

Wannan lamari dai na ci gaba da jawo suka ga baki daga sassa daban-daban na duniya inda ko a jiya dan takarar shugabancin Amirka Donald Trump wanda akewa kallon me kin jinin baki ya tofa nasa albarkacin bakin.

"Abin da ke faruwa a Jamus abu ne da tunani ba zai dauka ba, wannan kasa ce da ba ta san wannan matsalaba ta cin zarafin mata a baya suna zaune lafiya, amma yanzu da baki sama da miliyan suka shiga ga abin da ke faruwa".