Jamus za ta kara taka rawar gani a Afirka | Labarai | DW | 22.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta kara taka rawar gani a Afirka

Gabanin taron hadin gwiwar da Kungiyar EU da na Afirka za su yi a watan gobe, Jamus ta yi alkawarin kara tallafawa kasashen Afirka domin inganta dangantakarsu

Entwicklungsminister Gerd Müller Bangui Zentralafrika

Ziyarar Gerd Müller ministan raya kasa a Bangui

Gwamnatin kasar Jamus ta bayyana kara taimakon raya kasa da take bai wa kasashen Afirka, tare da bayyana nahiyar a matsayin wadda take cike da dama.

Wannan mataki ya zo kafin gudanar da taro tsakanin Kungiyar Tarayyar Turai da Afirka cikin wata mai zuwa a birnin Brussels na kasar Belgium.

Mahukuntan birnin Berlin na Jamus sun bayyana cewa taimakon zai yi tasiri wajen bunkasa ilimi da cibiyoyin ba da horo da kuma ci gaba mai dorewa a bangaren aikin gona, kamar yadda ministan raya kasashe na kasar ta Jamus Gerd Müller ya tabbatar.

Ministan ya kara da cewa ta daukan irin wannan matakan kasashen na Afirka za su sami irin bunkasar da ake bukata.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba