1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Jamus da Rasha

Binta Aliyu Zurmi
September 6, 2020

Ana ci gaba da tada jijiyoyin wuya tsakanin kasashen Jamus da Rasha a kan zargin da ake wa Rasha na saka wa madugun 'yan adawa Alexei Navalny guba.

https://p.dw.com/p/3i59E
Berlin I Heiko Maas
Hoto: Reuters/S. Loos

Dangantaka na kara tsami wanda ta kai Jamus yin barazanar sanya wa Rasha takunkumi, muddin ta ki bada hadin kai a binciken da ake yi.

A wata tattaunawa da ya yi da mujalar Daily Bild, ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya ce idan har Kremlin ta ce bata da hannu a cikin wannan lamarin to ta fito da kwararan shaidu domin kare kanta. Maas ya kara da cewa idan kuwa ba su yi haka ba cikin 'yan kwanakin nan da ke tafe to za su dauki matakan da suka dace.

A nata bangare Birtaniya ta ce Rasha na da tambayoyi da za ta amsa. A satin da ya gabata ne Jamus ta sanar da cewar ba makawa Alexei Navalny ya hadiyi gubar sinadarin Novichok mai sarke jijiyoyi.