Jamus za ta dauki yara 150 daga cikin ′yan gudun hijira Moria | Labarai | DW | 11.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta dauki yara 150 daga cikin 'yan gudun hijira Moria

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sanar da aniyarsu na daukar kananan yara 150 daga cikin wadanda gobarar sansanin yan gudun hijira mafi girma a nahiyar Turai na Moria da ke kasar Girka ya rutsa da su. 

Wannan na zuwa ne bayan da Firaiministan kasar Girkar ya bukaci taimako daga kasashen kungiyar EU.
Har wayau Jamus ta yi alkawarin kyautata rayuwar wadannan mutanen tare da samar musu matsuguni mai kyau.

Ministan harkokin cikin gidan Jamus Horst Seehofer ya sanar a wannan rana ta Juma'a cewar kasashen EU goma za su dauki kananan yara kimanin 400. Kungiyar ta tarayar Turai na shirin fidda sabbin yarjejeniya game da 'yan gudun hijira da ma yan ci-rani a nahiyar.