1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na fuskantar karancin ma'aikata

Abdourahamane Hassane
December 27, 2018

Rundunar sojojin Jamus Bundeswehr ta ce saboda karanci ma'aikata akwai yiwar ta dauki sabbin ma'aikata daga kasashen tarrayar Turai wanda ke da kwarewa ta fannin aikin likita da injiniyoyi na kimiyya da fusaha.

https://p.dw.com/p/3Agpz
Shugaban hafsan hasoshin Jamus Janar Eberhard Zorn
Shugaban hafsan hasoshin Jamus Janar Eberhard ZornHoto: picture-alliance/Tagesspiegel/M. Wolff

Shugaban hafsan hasoshin Jamus Janar Eberhard Zorn, ya ce kafin a aiwatar da shirin ya zama dole a kawo gyara ga dokar kasar da ke cewar kafin zama soji a runudnar ta Bundeswehr dole ne ya zamanto sai Bajamushi ne. Kasar Jamus wacce al'ummata ke tsuffa na fuskantar karancin ma'aikata da sannu a hankali.