1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta ci gaba da karbar 'yan gudun hijira

Gazali Abdou TassawaJuly 28, 2016

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi watsi da kiraye-kirayen yin watsi da siyasarta ta karbar 'yan gudun hijira da wasu 'yan kasar suka fara yi bayan hare-haren ta'addacin da suka faru a Jamus.

https://p.dw.com/p/1JXT2
Angela Merkel Porträt
Hoto: Getty Images/Gallup

Merkel ta bayyana wannan matsayi ne a lokacin wani taron manema labarai da ta shirya a wannan Alhamis.Takanas shugabar gwamnatin kasar ta Jamus Angela Merkel ta katse hutun da take yi ta dawo kan aiki domin shirya wannan taro manema labarai,domin kare manufofinta.Daga sukar da ta fuskanta daga waje dama a cikin jam'iyyarta dangane da siyasarta ta karbar 'yan gudun hijira wacce ta yi kamari bayan da ta tabbata cewar hare-hare biyu daga cikin hudu da kasar ta fuskanta a cikin kwanaki 10 na baya-bayan nan 'yan gudun hijira ne, daya dan Afganistan daya kuma dan Pakistan suka kaisu.Sai dai Angela Merkel ta ce tana kan bakanta na ci gaba da wannan siyasa ta bayar da mafaka ga 'yan gudun hijira domin yin watsi da ita tamkar nasara ce ga kungiyoyin 'yan ta'adda inda ta yi karin bayani tana mai cewar:

"Ta ce ''Yan ta'adda suna so su kauda hankullanmu ne daga abubuwa masu muhimmanci, suna so su raba kawunanmu,su kuma lalata mana yadda muke rayuwa dama tsarinmu na tausaya wa wadanda ke cikin bukata, suna so su haifar da gaba tsakanin mabambantan al'adu da addinai,mu kuwa muna adawa da wannan mataki"

Babu gudu babu ja da baya a game da karbar baki a cewar Merkel

'Yan gudun hijira sama da miliyan daya ne dai kasar ta Jamus ta bai wa mafaka a karkashin siyasar ta gwamnatin Angela Merkel da suna jin kai.Sai dai hare-haren ta'addancin da kasar ta fuskanta sun tayar da al'ummar kasar ta Jamus daga mafarkin da ta ke yi na ganin cewar ita ta tsira daga barazanar 'yan ta'adda. Masu adawa da wannan siyasa ta Merkel na ta faman kiraye-kiraye na ganin ta saurara matakan karbar bakin haure da 'yan gudun hijira a kasar. Dangane da irin wadannan korafe-korafe ma dai shugabar gwamnatin kasar ta Jamus ta ce ba ta da niyyar sauya ra'ayi:

Angela Merkel Bundespressekonferenz
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Kumm

"Ta ce “Kamar yadda na fada a shekarar da ta gabata, a yau na gamsu cewar tabbas za mu iya jurewa yanayin da ci gaban duniya ya haifar mana. Ina sake jaddadawa za mu iya kamar yadda muka yi watanni 11 da suka wuce, saboda haka za mu ga karshen kalubalen da muke fuskanta daga masu tsattsauran kishin islama, akwai matakai da muka tanada don ganin Jamus ta kasance cikin tsaro”

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta kuma bayyana cewar ba a siyasa da tsoro dan haka ta fito da wasu shawarwarin guda tara na fuskantar kalubalen tsaron da kasar take fuskanta da suka hada da daukar karin sabbin jami'an tsaro masu zaman kansu da kuma wani tsari na gaggauta shaida wa jami'an tsaro duk wasu mutanen da aka lura na da tsattsauran ra'ayin addini.Mutane 15 ne dai suka hallaka a yayin da wasu da dama suka jikkata a cikin jerin wasu hare-haren da kasar ta Jamus ta fuskanta a cikin kasa da kwanaki goma.