Jamus za ta bayyana rahoton farko kan cin zarafin mata | Labarai | DW | 11.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta bayyana rahoton farko kan cin zarafin mata

A yau Litinin ake sa ran hukumomin tsaron kasar Jamus za su bayyana rahoton farko mai cike da bayanai kan cin zarafin matan da wasu mutane suka yi a birnin Cologne.

Angela Merkel

Angela Merkel

A jajibirin sabuwar shekarar nan ta 2016 ne wasu mutane suka fada wa mata tare da cin zarafinsu yayin bukukuwan karshen shekara, inda wadanda aka ciwa zarafin fiye da 500 suka shigar da kara wanda ake ganin hakan zai kara sanyaya wa shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel gwiwa a fafutukar da take na baiwa mafi yawan 'yan gudun hijira mafaka a kasar.

Bayan ma dai taron da suka gudanar a birnin Cologne, 'yan kungiyar nan ta Pegida masu kyamar baki sun gudanar da wata zanga-zanga, inda suke nuna adawarsu ga 'yan gudun hijira da kuma shugabar gwamnatin ta Jamus wadda cikin wani jawabi da ta yi, Merkel ta nuna damuwarta kan abun da ya wakana inda ta ce hakan na nufin cewa batun takardar izinin zama cikin kasa, ko na samun karbuwa a matsayin dan gudun hijira zai haramta ga duk wanda aka samu ya na da hannu ko kuma ya yi cin zarafi ga matan kai tsaye.