1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta cimma matsaya kan 'yan gudun hijira

Ramatu Garba Baba
June 30, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus ta sha da kyar a kokarin ceto gwamnatin hadakar kasar daga wargajewa bayan da ta samu daidaito da kasashen Turai kan magance matsalar kwararar 'yan gudun hijira da ya zame ma ta babban kalubale.

https://p.dw.com/p/30aWe
Trump Merkel
Hoto: Picture alliance/AP Photo/M. Schreiber

Daman a watan gobe ne wa'adin da aka bai wa Merkel ke cika kan samar da mafita ko kuma ta fuskanci barazanar rushewar gwamnatin hadakar da aka kafa bayan da a ka kwashi dogon lokaci ana kai ruwa rana.

Yanzu za a soma mayar da 'yan gudun hijirar da suka shigo kasar daga wata kasar Turai, cibiyar da aka tanadar musu a yayin da Jamus  ke ci gaba da duba cancartasu na zama a kasar.

Tuni dai Merkel ta mika sakamakon wannan yarjejeniyar da ta cimma da wasu kasashen yankin goma sha hudu a gaban jagororin jam'iyyun hadakar. A zaman taron na jiya Juma'a na birnin Brussels an yarda a samar da wasu cibiyoyin karbar 'yan gudun hijira a wasu kasashen da ba na Turai ba.