1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: 'Yan sanda sun kai sumame

Zainab Mohammed AbubakarAugust 10, 2016

A cewar ofishin shigar da kara na gwamnatin Jamus, ana zargin mutanen ne da laifuka da suka danganci ta'addanci.

https://p.dw.com/p/1JfZ2
Deutschland Kooperation zwischen Sicherheitskräfte
Hoto: picture-alliance/kolbert-press/C. Kolbert

Jami'an 'yan sanda a Jamus sun kai sumame zuwa wurin aiki da gidajen wasu mutane uku, da ake zargi da shirin horar da mutane domin shiga Kungiyar IS, a cewar ofishin babban mai shigar da kara na gwamnati.Sai dai ba'a kama kowa ba.

Ana zargin daya daga cikinsu da tallafa wa kungiyar 'yan ta'addan na IS a bangaren kudi da sufuri. Sumamen na yau Laraba ya gudana ne a jihohin North Rhine-Westphalia da Lower Saxony.

Frauke Köhler ita ce kakakin babban ofishin shigar da kara na tarayya a birnin Kalsruhe:

" Ta ce binciken da muka gudanar ya nunar da cewar, mutanen uku 'yan Salafiyya ne. Sun bayyana cewar sun koyar da darussa na addini da Salafiyya, salon na yin jihadi ga mutanen da ke shirin barin Jamus, domin su samu damar shiga kungiyar 'yan ta'adda ta IS".Kafofin yada labaru na Jamus dai sun shaidar da cewar binciken ya gudana ne a garuruwan Duisburg da Dortmund da Düsseldorf da kuma Hildesheim.Jamus din dai ta dauki tsauraran matakan tsaro tun bayan har- hare biyu da suka auku a watan Juli, wadanda suka kashe masu kai harin su ka dai.